Pulis na fatan sayo 'yan kwalllo kafin a rufe kasuwa

Tony Pullis kociyan West Brom
Tony Pullis ya ce yana fatan sayo 'yan wasa kafin a rufe kasuwar 'yan kwallon

A cikin watan nan na Janairu Pulis ya dauki Jake Livermore daga Hulll City kan kudi fam miliyan 10.

Za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula ta nahiyar Turai da tsakar daren ranar Talata.

Pulis ya ce suna zawarcin 'yan kwallo kuma sun tanadi kudin saya amma babu su a kasa domin ba kowa ne ke son sallamarwa ba.

West Brom tana mataki na takwas a kan teburin Premier ta bana, an kuma fitar da ita daga gasar kofin FA, wanda Derby County ta doke ta.

West Brom, ta sayar da Saido Berahino ga Stoke City a cikin watan Janairu kan kudi fam miliyan 12.