Ƙa’idar rubutu

Rubutun harshen Hausa yana da ƙa’idojinsa da ke taimakawa wajen yin rubutun irin yadda za a karanta shi cikin sauƙi, a kuma fahimce shi cikin sauƙi.

Sanin yadda haruffan Hausar suke da kuma yadda ya kamata a yi amfani da su don yin magana a rubuce wajibi ne.

Don taimaka mana wajen kyautata rubutunmu na Hausa, za mu dinga kawo misalai na kurakuran da ake yi da yadda ya kamata a gyara su.

Kuskure

Daidai

‘Yan uwansu

Wasun su

Dan uwan

‘Yan’uwansu

Wasunsu

Ɗan’uwan

A karshen wata Yuli, wata majiya ta tseguntawa BBC wani abu.

A karshen watan Yuli, wata majiya ta tsegunta wa BBC wani abu.

Wato “tsegunta” daban (tunda aikatau ce a nan), “wa” kuma daban.

…sai malaman Budda suka reneta

…sai malaman Budda suka rene ta

Wato “rene” daban (tunda aikatau ce a nan), “ta” kuma daban.

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba