Dabarun Yin Rahoto Mai Kyau (Kashi na Ɗaya)

Aiko da rahoto yana bukatar matakai da ɗan dama. Wannan ya haɗa da farautar labarin shi kansa, musamman a ranar da babu wani muhimmin abu da ke aukuwa. Kana, yaya za ka shawo kan wanda ke da wani bayani har ya amince ya faɗa maka shi?

Yaya kuma za ka yi da labarin da ka samu da ɗumi-ɗumi? Wani kuma ƙalubalen shi ne na rashin ƙarfin intanet.

Dukkan waɗannan suna cikin abubuwan da Ishak Khalid, wanda ya daɗe yana aiko da rahotanni, ya fayyace mana a wannan bidiyo.

A cikin wannan kashi na farko, Ishaq ɗin ya fara ne da yin bayani a kan yadda yake samun labarai.

 

 

Latsa nan domin kallon kashi na biyu

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba