Yadda ake Tantance Gaskiyar Labari da Kare Majiyoyi

Waɗanne matakai ake ɗauka don tabbatar da ingancin labari? Yaya kuma ake tantance gaskiyar labari daga majiyar da ba ta da ƙarfi? Jimeh Saleh, Muƙaddashin Editan Sashen Hausa na BBC ya yi ƙarin bayani a kan waɗannan matsaloli.

Labarai sukan fito ne daga majiyoyi daban-daban, wasu waɗanda aka tabbatar da ingancinsu, wasu kuma ba su da tabbacin inganci.

Waɗanda ba su da ingancin sun haɗa da labarin da wani zai bayar amma babu wata shaida da za ta iya tabbatar da hakan, kai kuma ba ka da wakili a wurin da abin ya auku da zai iya binciko maka.

Wani lokaci kuma labari ne ka samu ta hanyoyin sada zumunta irin su Facebook da Twitter, shin za ka ka bayar da shi kai tsaye? A’a. Shi ma sai ka tabbatar da majiyar labarin da ingancinsa.

Wata matsalar kuma da kan taso ita ce ta mutum ya ba da labari mai muhimmanci amma kuma ba ya son a faɗi sunansa bisa tsoron abin da ka biyo baya.

Su ma a cikin wannan bidiyo, za ka ji hanyoyin da za ka bi ka tabbatar da ingancin irin waɗannan labarai.

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba