
Sunayen Muhimman Tabkunan Duniya
A wannan karon mun kawo maku sunayen muhimman tabkuna na duniya ne da suke da girma ko suka fi suna. Mun kuma kawo maku sunayen ƙasashen da ke da iyaka da waɗannan tabkuna don ƙarin fahimtar labarin ƙasa. Sulaiman Ibrahim Katsina na nan BBC ne ya tsara mana su.

A wannan karon mun kawo maku sunayen muhimman tabkuna ne na duniya da fassararu ko rubuta sunayensu da Hausa don ƙara sauƙin karanta su idan aka ci karo da su. Hakan zai inganta harshen na Hausa ta hanyar ƙara masa yawan kalmomi.
Haka kuma, kawo su zai inganta saninmu game da sassan duniya daban-daban. Bisa haka ne muka jera sunayen su ma ƙasashen da suka yi iyaka da waɗannan tabkuna.
Wasu tabkunan suna da girman gaske har ma ana kiran su teku. Ba mu kawo irin wadannan ba a jerin sunayen tabkunan. Mun bar su a cikin jerin sunayen manyan tekuna na duniya da muka gabatar maku a baya. Misali, Tekun Aral.
Wasu tabkunan kuma sun yi suna ne saboda muhallin da Allah Ya ajiye su, da albarkar da ake samu game da su ko hairanin da ke tashi a kewayensu.
Tabkin da ke sama shi ne ya fi girma har zuwa na ƙarshensu a ƙasa, wato Kibu da Nasir. Duk da cewa Kibun da Nasir ba su cikin jerin mafiya girma, mun dai sanya su ne saboda sun yi suna sosai a Afrika, inda masu sauraren mu suka fi yawa.
Lake |
Tabkin |
Kasashen kewayensa |
Superior |
Supiriya |
Amerika da Kanada |
Victoria |
Bikitoriya |
Tanzaniya da Yuganda |
Huron |
Huron |
Amerika da Kanada |
Michigan |
Mishigan |
Amerika |
Tanganyika |
Tanganyika |
Tanzaniya da Jumhuriyar Dimokuradiyar Kwango |
Baikal |
Baikal |
Rasha |
Great Bear |
Gret Beya |
Kanada |
Nyasa |
Niyasa |
Malawi, da Muzambik da Tanzaniya |
Great Slave |
Giret Sileb |
Kanada |
Chad |
Cadi |
Cadi, da Kamaru, da Nijar da Najeriya |
Erie |
Eri |
Amerika da Kanada |
Winnipeg |
Winipeg |
Kanada |
Ontario |
Ontariyo |
Amerika da Kanada |
Balkhash |
Balkash |
Kazakistan |
Vostok |
Bostok |
Antaktika |
Ladoga |
Ladoga |
Rasha |
Onega |
Onega |
Rasha |
Titicaca |
Titikaka |
Bolibiya da Peru |
Nicaragua |
Nikaraguwa |
Nikaraguwa |
Alhabaska |
Alhabaska |
Kanada |
Taymyr |
Taimir |
Rasha |
Turkana |
Turkana |
Etopia da Kenya |
Reindeer |
Rendiya |
Kanada |
Kati Thanda-Lake Eyre |
Kati Tanda |
Ostreliya |
Issyk-Kul |
Isikul |
Kirgiztan |
Urmiya |
Urmiya |
Iran |
Torrens |
Torensi |
Ostireliya |
Vanem |
Banem |
Suwidin |
Winnipegosis |
Winipegosis |
Kanada |
Albert (Mobutu Sese Seko) |
Albat |
Yuganda da Kwango |
Mweru |
Muweru |
Zambiya da Jumhuriyar Dimokuradiyar Kwango |
Nettilling |
Netilin |
Kanada |
Nipigon |
Inpigon |
Kanada |
Manitoba |
Manitoba |
Kanada |
Great Salt |
Babban Tabkin Gishiri |
Amerika |
Kioga |
Kiyoga |
Yuganda |
Qinghai / Kokonor |
Cingai |
Sin |
Saimaa |
Saima |
Finland |
Lake of the Woods |
Itace |
Amerika da Kanada |
Khanka |
Kanka |
Rasha da Sin |
Kivu |
Kibu |
Ruwanda da Jumhuriyar Dimokuradiyar Kwango |
Nasser |
Nasir |
Masar da Sudan |