Cikakkun Sunayen Tekunan Duniya

Akwai manyan tekuna na duniya da ake kira ‘ocean’ da Ingilishi, akwai kuma waɗanda ba su kai su girma ba a ɓangarori da dama na duniya da ake kira ‘sea’ da Ingilishi. Mu ma da Hausa, waɗanda ake kira ‘ocean’ ɗin muna kiran su ‘teku’. Waɗanda kuma ake kira ‘sea’, wasu mukan kira su ‘teku’ wasu kuma ‘bahar’, kamar yadda Sulaiman Ibrahim Katsina na nan BBC ya duba mana su.

Akwai manyan tekuna na duniya da ake kira ocean da Ingilishi, akwai kuma waɗanda ba su kai su girma ba a ɓangarori da dama na duniya da ake kira sea da Ingilishi.

Mu ma da Hausa, waɗanda ake kira ocean ɗin muna kiran su ‘teku’. Waɗanda kuma ake kira sea, wasu mukan kira su ‘teku’  wasu kuma ‘bahar’.

Kome dai ya dogara ne a kan yadda masu fassara suka fassara sunan tun a can baya ko kuma yadda masu amfani da kalmomin suka fi jin dadin faɗinsu.

Su ocean  guda biyar ne a duniya, don haka mun kawo su duka a wannan jaddawali. Waɗanda aka fi kira sea kuwa suna da yawan gaske, don haka mun kawo waɗanda suka fi fitowa a labarai kawai.

Idan har aka ci karo da wadda ba mu rubuta ba a nan, sai kawai a kira ta ‘tekun …….’

Akwai kuma masu suna biyu kamar Bahar Rum, wasu sukan ce, ‘Tekun Meditareniya’. 

Ocean/Sea

Teku/Bahar

the Adriatic Sea

Tekun Adiriya

the Aegean Sea

Tekun Ejiya

the Andaman Sea

Tekun Andama

the Arabian Sea

Tekun Arebiya

the Aral Sea

Tekun Aral

the Arctic Ocean

Tekun Akatik

the Atlantic Ocean

Tekun Atilantika

the Baltic Sea

Tekun Balti

the Barents Sea

Tekun Barant

the Bay of Bengal

Tekun Yankin Bengal

the Bering Sea

Tekun Berin

the Bering Strait

Mashigin Berin

the Black Sea

Bahar Asuwad

the Bosphorus Strait

Mashigin Basfaras

the Cape of Good Hope

Tekun Kudancin Afrika

Cape Horn

Tekun Kudancin Amerika

the Caribbean Sea

Tekun Karibiyan

the Caspian Sea

Tekun Kaspiya

the Dead Sea

Bahar Mayit / Matattar Teku

the East China Sea

Tekun Gabacin Sin

the English Channel

Yankin Ruwan Ingila

Guantanamo Bay

Tekun Yankin Guwantanamo

the Gulf of Aden

Gaɓar Tekun Adan

the Gulf of Aqaba

Gaɓar Tekun Aƙaba

the Gulf of Alaska

Gaɓar Tekun Alaska

the Gulf of California

Gaɓar Tekun Kalifoniya

the Gulf of Guinea

Gaɓar Tekun Gini

the Gulf of Mexico

Gaɓar Tekun Mekziko

the Gulf of Suez

Gaɓar Mashigin Suwez

the Gulf of Thailand

Gaɓar Tekun Tailan

the Gulf of Tonkin

Gaɓar Tekun Tonkin

the Indian Ocean

Tekun India

the Java Sea

Tekun Jaba

the Kara Sea

Tekun Kara

the Mediterranean Sea

Bahar Rum / Tekun Meditireniya

the North Sea

Tekun Arewa

the Pacific Ocean

Tekun Pasifik

the Gulf (not the Persian Gulf, nor the Arabian Gulf)

Gaɓar Tekun Arebiya da Pasha

the Red Sea

Bahar Maliya

the Sea of Galilee

Tekun Galili

the Sea of Japan

Tekun Japan

the Sea of Marmara

Tekun Màmara

the South China Sea

Tekun Kudancin Sin

the Southern Ocean

Tekun Kudu

the Strait of Gibraltar

Mashigin Jibiralta

th Strait of Hormuz

Mashigin Homuz

the Magellan Strait

Mashigin Magelan

the Strait of Malacca

Mashigin Malaka

the Taiwan Strait

Mashigin Taiwan

the Tartar Strait

Mashigin Tatar

the Yellow Sea

Rawayan Teku

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba