
Hukumomin Ƙwallon Ƙafa a Taƙaice
A labarin wasanni ana yawan rubuta sunayen hukumomin ƙwallon ƙafa. Wani lokaci ba dukkan sunan ake son rubutawa ba saboda ƙarancin wurin rubutun. Misali, idan za a rubuta kan labari ko a inda za ai ta maimaita sunan a cikin dogon labari. Taƙaitawar za ta sauƙaƙa karatu, ta rage ƙosawa. Sulaiman Ibrahim Katsina na nan BBC, ya tsara mana yadda za a rubuta sunayen irin waɗannan hukumomi a taƙaice.

Taƙaice |
Cike |
WASANNI |
|
HUKKAB |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Biritaniya (FA) |
HUKKAD (FIFA) |
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) |
HUKKAF (KAF) |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Afrika (CAF) |
HUKKAG |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ghana (GFA) |
HUKKAK |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Kamaru (FECAFOOT) |
HUKKAKA |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Kudancin Amerika (CONMEBOL) |
HUKKAN |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Najeriya (NFA) |
HUKKANI |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijar (FENIFOOT) |
HUKKAO |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Oshiniya (OFC) |
HUKKAS |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Asiya (AFC) |
HUKKAT (YUWEFA) |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Turai (UEFA) |
HUKKATSAK |
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Arewa da Tsakiyar Amerika da Karibiyan (CONCACAF) |