Salo

BBC tana da salonta na nuna gogewa a aiki. Hakan ya haɗa da tabbatar da bai wa kowane ɓangare a muhawara damar faɗin albakin bakinsa. Wanda kuma aka kasa samu a faɗi hakan. Akwai kauce wa ashariya ko cin mutuncin wani. Lalle ne a tabbatar da sahihancin labari kafin a watsa shi. Akwai lura don kada a watsa abin da zai haifar da tarzoma. Akwai kuma sigar yadda ake ba da labari shi kansa, a rediyo, ko talabijin ko kuma intanet.

Kuskure

Daidai

A shirin safe da na hantsin Lahadin bayan muhawarar ‘yan takarar gwamnan Kano, an saka kaɗan daga cikin tambayoyin da aka tsakuro.

A ƙarshe sai aka ce, “A nan muka kawo ƙarshen wannan muhawara, don haka zan ba waɗannan ‘yan takara kowa minti guda domin ya yi jawabinsa na ban kwana.”

Amma sai aka saka muryar mai takara ɗaya tak.

Bai kamata a saka muryar mai takara ɗaya tak ba. Wani zai iya ganin ba a yi masa adalci ba.

Kamata ya yi ko dai a saka su duka kamar yadda aka ji muhawarar ranar Asabar, ko kuma in ba lokaci, kada a saka ko ɗaya.

A kullum BBC tana ƙoƙarin ganin ta kawar da duk wani rashin adalci ko alamarsa daga cikin shirye-shiryenta.

Yanzu ƙarfe uku da rabi ne saura minti sha biyar a Najeriya da Nijar.

 

Yanzu ƙarfe uku da kwata ne a Najeriya da Nijar.

Ƙarfe kaza ake iya haɗawa da saura kwata, amma banda rabin awa.

To ƙarshen shirin ke nan, amma bari na bar ku da Muhammad Abdu Mamman Sikipa ɗauke da labarin wasanni.

 

Bai kamata a rufe shiri da wani dogon rahoto ba. Akwai buƙatar bayan rahoto a ji sunan wanda ya yi shi da kuma daga inda ya yi shi. Sannan a rufe tasha da sunan mai gabatarwa, da wanda ya shirya shiri, da kuma sunan tashar.

Mai sauraron da ba da shi aka fara rahoton ba, zai sami cikakken bayani ke nan, na tashar, da rahoton da shirin. Duk waɗannan ba za su samu ba idan aka ƙare da dogon rahoto.

Amma idan ‘yan daƙiƙoƙi ne suka rage na wani sauti, aka yi sallama cikakakkiya, to za a iya barin mai sauraro da ɗan abin da ya rage na sautin.

Darajar Dalar Amurka da kudin peso na kasar Mexico ta fadi yayin da kasuwar shunku ta Dow ta yi asarar maki 650

Darajar kuɗaɗen dalar Amurka da peso na Mekziko ta faɗi yayin da kasuwar shunku ta Dow ta yi asarar maki 650

Ana ma iya cire ‘kuɗaɗe’ a ce dalar Amurka da peso na Mekziko. Tunda galibin masu iya karantawa sun san dala, za su kuma iya fahimtar peso a cikin wannan jumla

Kamata ya yi a rubuta ’peso’ kamar yadda aka rubuta ‘dala’. Idan kuma kuɗaɗen kawai aka ce ba a ce daraja ba, sai a ce sun faɗi. Misali: (Kuɗaɗen) dala da peso sun faɗi ….

Wata mata da ta zo wannan lambu, ta zura ido yadda ta ga waɗannan furanni. Ta cika da abin mamaki.

“…ta cika da mamaki.” Ba a cika da abin mamaki. Sai dai à iya cewa, “wane mai abin mamaki”.

Kama daga rashin isasshen abinci da ruwan sha da sauransu

In aka ce ‘kama daga...’ ya kamata a ƙare da ‘zuwa ga…’. Misali: Kama daga riguna zuwa ga sàfa da takalma.’

Duk wani kyakkyawan kare yana da ranarsa

Ko kare ma da ranarsa

Muna yi wa shugaban kasar Najeriya kashedi ne ya daina …

“Muna yin hannunka mai sanda ne ga ...” ko “Muna kira ne ya yi hattara” (Su suka fi dacewa da abin da mai magana ya faɗa, da ya ce, “It is just a to caution the President …”)

Ƙanƙantar shekaru

Ƙarancin shekaru (an fi cewa abu yana da ƙanƙanta in bai da girma.

An tabka shi kotu

“An maka shi kotu” (Ba a tabka mutum kotu, amma za a iya tabka shari’a). An fi amfani da “tabka” a kan wani abin da aka jima ana yi ko ya yi tsanani. Misali, “An tabka muhawara”, “An tabka ruwa”.

Wàne ya yi mana fashin baƙI

Wàne ya bayyana mana fahimtarsa (Ko ga abin da aàne yake gani d.s. ‘Fashin baƙi ba salon BBC ba ne)

Ga rahoto wàne

Wannan na nufin shi ne ya yi rahioton da kansa

Ga rahoton da wane ya haɗa mana

Hakan na nufin daga rahotanin wasu ne ya harhaɗa ya yi nasa

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba