Ruɗu

Mai sauraro ko karatu zai shiga ƙila-wa-ƙala idan bayanin da ake yi masa bai fito ƙarara ba. Hakan kan auku ne idan kana magana a kan mutane biyu ko fiye, ko abubuwa biyu ko fiye, amma ka kasa fayyace wanda kake nufin ya yi abu ko wanda abu ya sama. Misalin haka shi ne: “Amadu ya je wajen sabon abokinsa wanda har yanzu bai iya faɗin sunansa ba.” A nan babu tabbas a kan wanda bai iya faɗin sunan ɗayan ba.

Kuskure

Daidai

Ƙabilar baha’i

Mabiya addinin baha’i

Baha’i ba ƙabila ba ce addini ne.

Kasancewarka naƙasa

Kasancewarka mainaƙa/naƙsasshe

Kumurcin maciji

Kumurci

(Kumurci maciji ne don haka ƙarawa da maciji almubazzarancin kalmomi ne)

“Dakarun gwamnatin Siriya ta watsa luguden wutar da ya halaka, wato ta halaka mutane da dama…”

Akwai ruɗu a wannan jumla. Babu tabbacin abin da ake nufin cewa.

Wakilin BBC ya ce, “Gwamnatinn Siriya ta aiwatar da mafi munin harin da ta kwashe shekaru ba ta kwance ba a Guta.”

Ma’ana ba ta fito ƙarara ba. A jumlar ba a san abin da ake nufi da “…mafi munin harin da ta kwashe shekaru ba ta kwance ba.”

Hukumomin Katalan

Hukumomin Kataloniya – ita ce fassarar Catalonian authorities

Idan aka ce Nigerian authorities ai za a fassara shi ne da Hukumomin Najeriya ko, ba Hukumomin Najeriyan ba.

Idan aka ce Ghanaian authorities Shi ma Hukumomin Gana za mu ce ko?

Haka kuma idan aka ce Afghan authorities, cewa za mu yi Hukumomin Afganistan ba na Afgan ba.

Swiss (account, franc, authorities) duk na Suwizalan ke nan.

Kaso ɗaya cikin biyar na mutane milyan ashirin da biyu da ke Jumhuriyar Kamaru na amfani da harshen Turanci.

Kaso ɗaya cikin biyar na mutane milyan ashirin da biyu da ke Jumhuriyar Kamaru na amfani da harshen Ingilishi.

Mutanen Nijar suna kiran Faransanci, Turanci. Su ma mutanen Najeriya suna kiran Ingilishi, Turanci. Don haka, duka Faransanci da Ingilshi Turanci ne a wajen masu magana da su, a Nijar ko a Najeriya.

Lalle ne a kira English Ingilish, a kuma kira French Faransanci inda duk ake batu a kan harsunan biyu ko kuma inda ke da yiwuwar samun ruɗu.

 

Tarzomar Boko Haram

 

Rikicin Boko Haram

Tarzoma tashin hankali ne, ko hargitsi ko husuma ta ɗan lokaci a wani wuri.

Rikici kuwa ya fi ƙunsar duk wata matsala irin wannan mai wuyar sha’ani.

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba