Mufuradi da Jam’i

Idan ba ka yi amfani da mufuradi ko jam’i ba a inda suka dace, za ka iya sauya ma’anar labari. Kada ka ce, “Gidaje ya ginu” maimakon “Gidaje sun ginu”. Idan ba ka yi aiki da ƙa’idar nahawu ba, za ka iya riikita mai sauraro ya kasa gane shin gidaje kake son ka ce ka manta ko kuwa gida ɗaya ne tal? Bai wa kowace kalma ko harafi haƙƙinsu zai taimaka wajen isar da saƙonƙa ba kuskure.

 

Kuskure

Daidai

Duk da tsattsauran matakan tsaro da ake fuskanta

Duk da tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka.

Na farko, tunda an an ce ‘tsattsauran’ to sai a ƙare da mataki. Wato mufuradi ya siffanta mufuradi. Jam’i ya sifanta jam’i. Misali: tsauraran matakai.

Kada a ɗauki rigar mutum guda a ce za a sa wa tarin mutane ko kuma akasin haka.

Ana bayyana damuwa game da yadda matasa suke mantawa da mummunan haɗurran da ke tattare da cutar.

Idan haɗari guda ne, sai a ce ‘mummuna’, idan kuwa sun zarce ɗaya sai a ce ‘munana’.

Kamata ya yi a koyaushe a lura da adadi, mufuradi ko jam’i, domin a haɗa shi da jam’in da ya dace da shi.

Faɗuwar darajar kuɗin ƙasa ta sa farashin kayayyaki sun tashi

Faɗuwar darajar kuɗin ƙasa ta sa farashin kayayyaki ya tashi

Tsofaffin mayaƙan ‘yan tawaye da suka ajiye makamansu a Abiri Kos sun toshe hanyoyi a Bouake, wanda shi ne gari na biyu mafiya girma a ƙasar.

Tsofaffin mayaƙan ‘yan tawaye da suka ajiye makamansu a Abiri Kos sun toshe hanyoyi a Bouake, wanda shi ne gari na biyu mafi girma a ƙasar.

Tunda gari ɗaya ne ba garuruwa aka ce ba, bai yiwuwa a yi masa jam’i.

An fafata tsakanin ‘yan takara mafi farin jini.

An fafata tsakanin ‘yan takara mafiya farin jini.

Tunda ad/adin ‘yan takarar na jam’i ne, lalle ne a siffanta shi a jam’ince.

Sun bayyana kalamai maras daɗi kan rasuwarsa.

Sun bayyana kalamai marasa daɗi kan rasuwarsa.

Tunda adadin kalamai na jam’i ne, lalle ne a siffanta shi a jam’ince.

Kura-kurai

Kurakurai. Jam’in da ya ƙare da ‘ai’ ba a sa masa gadà. Don haka, bam = bamabamai, kutuki = kutakutai, gungume = gumagumai.

Su kuwa kalmomin da aka maimaita ba tare da wani sauyi ba ana yi masu gadàr. Misali: manya-manya, lokaci-lokaci, filla-filla.

Ko a ranar Jumma’ar da ta gabata an sake kai wasu hare-haren a wurare biyu a cikin garin na Maiduguri da ya halaka mutane aƙalla shidda, ciki har da maharan

Ko a ranar Jumma’ar da ta gabata an sake kai wasu hare-haren a wurare biyu a cikin garin na Maiduguri da suka halaka mutane aƙalla shidda, ciki har da maharan.

‘Hare-hare’ jam’i ne na ‘hari’, don haka ba za a ce ‘ya’ ba, sai dai a ce, ‘suka’.

Ɗaya daga cikin Firaministan Biritaniya

Ɗaya daga cikin Firaministocin Biritaniya – Daga cikin jam’i ne, ba daga cikin ƙwara ɗaya ba

Sannan a cikin labarin na sama na Siriya, an ce “wani ayarin…” aka ƙare da “sun sake…”, aka gwamutsa ‘mufuradi’ da ‘jam’i".

Sai dai a ce “wani ayari….ya”. Jam’i ana haɗa shi ne da jam’i ɗan’uwansa. Mufuradi kuma da mufuradi

Hare-haren ya raba dubban mutane da muhallinsu

“Hare-haren sun raba dubban mutane da muhallinsu”. Yawan fara magana da jam’i tare da ƙarewa da mufuradi yana cikin matsalolin da aka fi ji a kafofin watsa labarai kamar wanda muka rubuta a hagu. Kamata ya yi ƙwarya ta bi ƙwarya. In ka faɗI jam’i to yi amfani da “sun”. Misali: Motoci sun wuce.

Wani ɗan shekaru …..

“Wani ɗan shekara…” Ko da yake amfani da jam’i yana da matukar muhimmanci a inda ya dace, akwai kuma inda in aka yi amfani da shi sai ka ji bambarakwai, amma ba a cewa ba daidai ba ne. A tambayar shekaru, misali, Bahaushe bai faye amfani da jam’in ba. Zai ce ne, “Shekararka nawa da haihuwa?” In kuma ka ce, “Shekarata 30 da haihuwa, ba za a ce jumlar ba ta yi daidai ba.” Abin da ma ya fi dacewa da al’adar Bahaushe ke nan.

Domin tantance hanyoyi mafi a’ala

Mafiya a’ala (tunda an ce hanyoyi, wato an yi jam’i lalle a ce ‘mafiya’)

Wasanni ya kankama

Wasanni sun kankama (wasanni jam’i ne na wasa, don haka lalle a ce ‘sun’ maimakon ‘ya’)

A kan yadda bukukuwan Kirsimati ya gudana a Kamaru

Suka gudana (ai bukukuwa ake ce ba buki ba)

Kuna sauraren waɗannan shirye-shirye ne

‘Kuna sauraren wannan shiri ne’ ya kamata a ce tunda shiri guda ne, na Safe, Hantsi, Rana ko Yamma. Ba shirye-shirye da yawa ba ne a cikin shiri guda

Shure-shure ba ta hana mutuwa

Shure-shure ba ya (bai) hana mutuwa ake cewa

Wasu cikakken bayanai

‘Wasu‘ kalma ce ta jam’i, haka ma ‘bayanai’, don haka ba za a ce ‘cikakken’ ba, saboda ita kalma ce mufurada. Sai dai a ce ‘Wasu cikakkun bayanai’

Bindigu

‘Bindigogi’ shi ne jam’in ‘bindiga’ ba ‘bindigu’ ba

‘Yan takarkaru

‘Yan takara (a jam’in ɗan takara ɗan ne za a sauya zuwa ‘yan)

Labarurruka

Labarai

Mataye

Mata (ya fi sauƙi)

Fatuttuka

jam’iyyu (ɗaya kuma ‘jam’iyya’)

Balabalai

Ƙwallaye (ɗaya kuma ‘ƙwallo’)

Kulubluka

Kulob-kulob

Suna mai cewa

Suna masu cewa (‘suna’ jam’i ne na ‘yana’ ko ‘tana’ don haka sai dai a ce ‘màsu’)

Bayanan da na tattara shi ne

Bayanan da na tattara su ne (‘bayanai’ jam’i ne na ‘bayani’ don haka sai dai a ce ‘su ne’)

 

Abubuwa Biyu Kacal da Za su Gyara Hausarka

Akwai abubuwa biyu da har waɗanda Hausa ta haifa gaba da baya suke yawan kuskure a kai idan sun zo magana da Hausar. Suna kuma yawan maimaita waɗannan kurakurai da ake kama sun da su.

Za kai ta yawan jin su daga bakin ma’aikatan kafofin labarai da mutanen da suke tattaunawa da su.

Idan suka gyara waɗannan ababe biyu, za su inganta Hausarsu ƙwarai da gaske. 

Kurakuran guda biyu

Waɗannan wurare biyu kuwa su ne:

 1. Jirkita jinsi, wato mayar da abu namiji ya koma mace ko akasin haka
 2. Jirkita adadi, wato mayar da jam’i ya koma mufuradi (abu guda)

Bari mu bi su ɗaiɗaya don gane yadda ake yin waɗannan kurakurai da kuma yadda za a gyara su. A nan za mu yi batu ne a kan Jirkita adadi.

Jirkita adadi

An fi jirkita adadin jam’i zuwa na mufuradi a wajen magana. Misali, kwanan nan a wani shiri na rediyo na ji wani ya ce, “Muna mai alfahari,” bayan kuma tunda ya ce, ‘Muna…’ ya yi amfani da kalmar jam’i ke nan, kamata ya yi ya ƙare da ‘…masu’, ba ‘…mai’ ba.

Wani zai iya cewa, “Gidajen sinima ya yi yawa a garin nan.” Sai dai tunda ya ce gidaje, kamata ya yi ya ƙare da cewa, “…sun yi yawa a garin nan.” Domin ‘gidaje‘ jam’i ne na ‘gida’.

A takaice dai a kula, kalmar jam’i, a haɗa ta da kalmar jam’in da ta dace da ita. Ta mufuradi kuma, a haɗa ta da ta mufuradi ‘yar’uwarta.

Misali:

Muna farin ciki da taryar da aka yi mana.

Idan mutum ɗaya ne:

Ina farin ciki da taryar da aka yi mani

Kalmomin jam’i na mutane da dabbobi

 1. muna, kuna, suna
 2. waɗannan, waɗancan, waɗansu, wasu, ku
 3. maza, màtà, yara, samari,  ‘yammata
 4. malamai, dalibai, ‘yan-sanda, gandirebobi
 5. shanu, raƙumma, awaki, tumaki, tsuntsaye

Kalmomin jam’in abubuwa

gonaki, gidaje, rafuka, ramu, turaku, idanu, hannuwa, d.s.

Wasu wakilan sunaye na jam’i

 1. mun, muna, kun, kuna, sun, suna
 2. muke, kuke, suke
 3. za mu, za ku, za su

A taƙaice dai, duk kalmar da aka yi amfani da ita ta jam’i, a tabbatar an haɗa ta da ta jam’in da ta dace da ita. Ƙwarya ta bi ƙwarya.

A mufaradi babu matsala sosai, ba safai akan mayar da mufuradi jam’i ba. Amma shi ma a yi hattara. A tuna a haɗa namiji da ‘ya’ mace kuma ‘ta’, ‘ka’ ko ‘kin’, ‘kai’ ko ‘ke’, ‘shi’ ko ‘ita’, d.s.

Misali:

 1. Yaro ya zo
 2. Yarinya ta zo
 3. Zaure ya cika
 4. Rumfa ta cika

Kira

Abin da muka bayyana a sama game da wannan matsala da ke cikin biyu da aka fi yin kuskure a kai na jirkita jinsi da jirkita jam’i, a taƙaice ne kawai.

In kuna sha’awar ƙara inganta yadda ya kamata ku sarrafa harshen Hausa, sai ku nemi malami ko littafan da suka dace don yin hakan.

Don karanta bayanin jirkita adadi, sai a je shafin Jinsi: http://bbc.in/1AMkFGs

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

 • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
 • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba