Manyan haruffa

Ana amfani da manyan haruffa a kan baƙin farko na abubuwa da dama. Sunan mutum yana farawa da babban baƙi. Haka sunayen abubuwan fasaha kamar su littafi, ko fim, ko waƙa. Haka sunayen ranaku, da watanni da bukukuwa irin su Salla da Kirsimati. Haka kuma sunayen hukumomi. Misali: Hukumar Lafiya ta Duniya

Kuskure

Daidai

Wani mai sharhi, malam Mannir Dan Ali

Malam Mannir Dan Ali (Ana farawa ne da babban baƙi idan za a haɗa kalmar ‘malam’ da sunan mutum)

A sashen Hausa

Sashen Hausa (Sunayen littafai, da fim da muhimman wurare, ana soma rubuta kowace kalmarsu ta suna ta farko da babban baƙi. Misali: Majalisar Ɗinkin Duniya)

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba