Lafazi

Idan kana watsa labarai ko magana kai da wani ko wasu, lalle ne ka tabbatar ka faɗi kalmomin da kake amfani da su daidai da yadda ƙa’ida da al’ada suka tabbatar, sai fa in kana da wani ƙwaƙƙwaran dalili da za ka iya kawowa na ƙin yin hakan. Lafazi ba daidai ba zai iya sauya ma’ana. Misali, tsakanin gàbà da gabá. Su ma sunaye daga wasu baƙin harsunan suna da haɗari. Za ka iya sanin ‘yan ƙa’idojin furta wasu harsunan in ka yi bincike. Wasu kuma tilas ka koye su a lokacin da ka same su.

Kuskure

Daidai

Suna zanga-zanga ta kin jinin Shugaba Abdulaziz Butelefki

Suna zanga-zanga ta ƙin jinin Shugaba Abdulaziz Butefiliƙa.

A yi ƙoƙarin faɗin sunaye daidai.

Wani lokacin har ma abokan aikinmu ba ma faɗin sunayensu yadda suke kiran kansu.

In ba ka da tabbas, ka tambayi mai sunan yadda yake son a kira shi.

Kyawawu

Kyawawa ake cewa

Honourable

Onarabul – Ba a furta sautin ‘h’ a wannan kalma ta Ingilishi, ka ɗauka tamkar kalmar ta fara ne da ‘o’. Akwai wasu kalmomin na Ingilishi ‘yan’uwanta da su ma ba a furta sautin ‘h’ ɗinsu, irin su ‘heir’, da ‘honest’, da ‘hour’. Sai kuma kalmar ‘herb’, wadda ita ana furta ‘h’ ɗinta a Turancin Ingila amma ba a furta ‘h’ ɗinta a Turancin Amerika.

Wasu kan karanta saa’a ta lokaci a kamar sa’a ta tsara.

Duk da yake a rubutun Hausa ana rubuta sa’a ta lokaci da ta samun nasara da tsara bai ɗaya kamar haka ‘sa’a’, wadda ke nufin lokaci ko samun wata nasara, duk ana jan gaɓar farko ne kamar haka: ‘saa’a’. Wadda kuma ba a ja gaɓar farko ba, tana nufin wanda kuke kusan shekaru ɗaya ke nan, wato ‘tsara’.

A labarai an kira biranen Faransa na Marseille a matsayin Maksel, da kuma na Nice a matsayin Nayis.

Kwatankwacin yadda ake kiran sunan Marseille shi ne “Marsè(ye)”, na Nice kuma “Nis”

Lalle a nemi sanin yadda ake faɗin sunayen da ke cikin labarai ta tambayar wanda ya sani, ko binciken ƙamus ko kuma intanet.

Cibok ko Ciɓok?

‘Cibok’ shi ne yadda ‘yan garin ke kiransa

‘Ch’ a Faransanci

Daidai take da ‘sh’ a Hausa. Idan Bafaranshe ya rubuta ‘Aicha’ yana nufin ‘Aisha’ ke nan. Kada ka je ka ce ‘Aica’.

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba