Kuskure a labari

Rashin fahimtar labari yana haddasa kuskure. Haka jinsin wanda ke cikin labarin, tun da Hausa na buƙatar fayyace jinsin mai magana. Misali. za ka iya ɗaukar sunan Hilary Benn a matsayin na mace saboda ka san Hillary Clinton ta Amerika mace ce, amma in da za ka bincika, za ka iske cewa ashe Hilary Benn namiji ne, tsohon minista a Biritaniya. Hausa ma tana da Gambo namiji da Gambo mace. Yarbanci ma yana da irin nasa.

Kuskure

Daidai

To yanzu dai ƙarfe bakwai ne saura minti goma sha shida a Dogon Jeji da ke jihar Sakkwato  a Najeriya…

To yanzu dai ƙarfe bakwai ne saura minti goma sha shida a Dogon Daji da ke jihar Sakkwato  a Najeriya…

Na tambayi Sakkwatawa sun ce, Dogon Daji ake cewa kamar yadda na zata.

Yanzu Sa’udiyyar ta ce ta kammala wannan tankaɗe da rairaya. An miƙa wa gwamnatin ƙasar fiye da dala milyan ɗaya, kusan da ma adadin kuɗin da gwamnatin ƙasar ta ce tana nema.

Dala bilyan ɗari ne ($100b.) ba milyan ɗaya ba.

A dinga hattara sosai da adadi don gudun yin gagarumin kuskure irin wannan.

“Majalisar ­ Ɗinkin Duniya  'ta yi wa ɗan Nigeria coge'

Wannan kan labari ba daidai ba ne.

A hirar da aka yi da wanda ya yi nasarar cin kyautar kula da ‘yan gudun hijira, kuma yake jiran kuɗin nasa, ya ce ne jinkiri ne ake samu bisa irin ƙa’idojin da Majalisar Ɗinkin Duniyar ke bi kafin ta ba da kuɗi, to yaya za a rubuta kan labari da ke cewa wai ta yi wa ɗan Najeriya coge?

“Wannan shi ne iyakar wulakanci da kuma rashin rashin ya kamata, wanda ba a taba ganin irinsa ba a jihar Kaduna."

"Wannan shi ne iyakar wulakanci da kuma rashin sanin ya kamata, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a jihar Kaduna."

Kasuwar baje kolin duniya ta jihar Kano ta fara ci a karo na 37. Kuma Cibiyar Bunkasa Ciniki, da Masa’antu, Ma’adinai da Aikin Gona ce ta shirya.

Sai dai har aka kammala wannan rahoto ba a faɗi ko a wane gari ne a jihar Kanon kasuwar ke ci ba. A Gezawa ne, ko Warawa ko kuma Rimin Gado? An bar waɗanda ba su sani ba da ƙila-wa-ƙala maimakon sanin takamaiman wuri.

Yau dai ranar Litinin an kuma yi wasanni shidda a gasar Firimiya, inda aka ci ƙwallaye talatin da biyu a cikin raga

Zuwa yau Litinin an yi wasanni shidda a gasar firimiya, inda aka ci ƙwallaye talatin da biyu a cikin raga. Yadda aka rubuta da farko zai iya sanya mai saurare zaton cewa a yau Litinin ɗin ne aka yi wasannin. Bayan kuwa ana batu ne a kan wasannan da aka yi kafin safiyar ta Litinin lokacin da ake waɗannan labarai.

Ya ce, “Mai abu da abinsa. Haƙiƙa nasarar Barazil ba ta ba mu mamaki ba, ganin cewa ita ce kan gaba wajen samun lambobin yabo a gasar.”

Da bai kamata a karanta wannan saƙo ba, ko kuma in har an karanta, ya kamata a yi wa wanda ya aiko shi gyara domin Barazil sam ba ta cikin na gaba wajen samun lambobi. Barazil ta goma-sha ce a yawan lambobin.

Wani ayarin Majalisar Dinkin Duniya sun sake kai kayan agaji a garin Madaya, wanda ‘yan tawaye suka yi wa kawanya. Kifraya da Alfu’a, wadanda su ma ‘yan tawaye suka yi wa kawanya.

‘Madaya’ a lokacin da aka yi wannan labari sojin gwamnati ne suka yi masa ƙawanya ba na ‘yan tawaye ba.

Kan ƙoƙarin kare wasu ‘yan ƙasar Iran masu hannu cikin lamarin

Kan ƙoƙarin kare wasu ‘yan ƙasar Iran da ake zargi da hannu a lamarin. (A wannan hali, kotu ce za ta iya tabbatar da ko suna da hannu ko a’a, don haka sai dai a ce ‘zargi’)

Ƙasashen biyu (Sabiya da Kuroshiya) da ke maƙwabta da Yugoslabiya

Ba sa maƙwabtaka da Yugoslabiya. Illa dai su duka yankuna ne na tsohuwar ƙasar ta Yugoslabiya

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba