Fassara

Lalle mai fassara ya tabbatar da cikakkiyar fahimtar harshen da yake fassara daga gare shi da kuma wanda yake fassarar zuwa gare shi. Shi ma sanin al’adun masu magana da harsunan biyu zai taimaka wajen rage kuskure, domin al’ada takan sanya ma’anar wasu kalaman ta saɓa wa fassarar kalmomin da ke cikinsu. Kana ya kamata ka san inda za ka iya yin fassarar kai-tsaye da kuma ta ma’ana kawai.

Kuskure

Daidai

Hukumar ta ce aikinta shi ne ta ceto al’umma a duk yanayi na rashin tabbas da suka tsinkayi kansu.

Hukumar ta ce aikinta shi ne ta ceto al’umma daga duk wani yanayi na rashin tabbas da suka sami kansu.

‘Tsinkayi’ na nufin hangen abu, don haka ‘suka sami kansu’ ne ya fi dacewa.

Kalaman nasa dai na zuwa ne wasu ‘yan makwanni bayan da Amerika ta nuna amincewa da ikon da Isra’ilar ta ce tana da shi a kan tuddan Golan, wanda Isra’ilar ta ƙwato daga Siriya.

Kalaman nasa dai na zuwa ne ‘yan makwanni bayan da Amerika ta nuna amincewa da ikon da Isra’ilar ta ce tana da shi a kan tuddan Golan, waɗanda isra’ilar ta ƙwace daga Siriya.

 

Tunda an ce ‘‘yan makwanni’ ba sai an ƙara da ‘wasu’ ba. Taƙaita kalmomi yana cikin ƙa’idojin rubutu nagari.

Sannan tunda an ce tuddai, kalma ce ta jam’i, shi ya sa ba za a ce ‘wanda’ ba, sai  dai ‘wad’anda’.

Idan aka ce ‘wanda Isra’ilar ta ƙwato’ tamkar  da ma tuddan nata ne ke nan sai ta ƙwato abinta. Sai dai a ce ‘wanda Isra’ilar ta ƙwace,’ abin da shi ne ya auku.

I think most of us if we saw a photo of someone with black face or in a kkk garb….

Ina ganin akasarinmu in muka ga wani da baƙar fuska ko sanye da kayan ƙawa…

Ma’anar “‘kkk garb’ shi ne, ‘tufafin ‘yan ƙungiyar kkƙ”. Don haka, a iya cewa, “Sun yi shiga irin ta ‘yan ƙungiyar kkk”.

Lalle ne idan aka ci karo da wani abu baƙo a bincika ma’anarsa. Idan kalma ce, a duba ƙamus, idan kuma wani abu ne daban, a duba shi a shafin bincike irin su google don sanin ma’anarsa da bayani game da shi.

Janar Mansur Dan Ali Mai Murabus.

Janar Mansur Dan Ali Mai Ritaya.

Murabus na nufin rubuta takardar barin aiki tun lokacin ƙarewar aikin bai zo ba.

Ritaya kuma na nufin barin aiki bayan kaiwa ƙarshen shekarun aiki na dindindin ko kuma hukuma ta yi wa mutum ritaya ko da lokacin bai yi ba.

Don haka, gara a ce mai ritaya, sai fa in an tabbatar murabus iɗn ne ya yi.

Ko kuma idan sam babu tabbas, to gara a ce tsohon Janar, ko Sufeto-Janar an huta ke nan.

… a kasuwar Wall Street a Amurka, inda hajoji suka rage daraja da kashi biyu cikin ɗari na farashinsu.

… a kasuwar Wall Street a Amurka, inda hannayen jàri suka rage daraja da kashi biyu cikin ɗari na farashinsu.

Ya ambato dozuna na makarantu da aka rufe..

 

Ya ambato gwammai na makarantu da aka rufe…

Dozuna ba Hausar da aka saba da ita ba ce.

An kuma ƙwace kayayyakin more rayuwa fiye da na dala milyan dubu ɗari biyu da saba’in a gidan tsohon shugaban (tsohon Firaministan Malesiya, Najib Razak)

 

Duk sa’ar da aka ce milyan dubu, to an ce bilyan ke nan. Don haka a wannan labari, dukiya ta kai kimanin milyan ɗari biyu da saba’in ce, amma an maida ta bilyoyin fitar hankali saboda sanya kalmar dubu da aka yi.

Ko a inda ma kuɗi suka kai bilyan ɗin, to gara a yi amfani da ita maimakon a ce milyan dubu don maganin ruɗani

Amma a wannan labarin dai kuɗin ba su kai milyan dubu ba. Don haka, ba su kai bilyan ɗaya ba.

‘Yan sanda a Afrika ta Kudu sun ce sun gano gawar wani masanin shuke-shuke.

‘Yan sanda a Afrika ta Kudu sun ce sun gano gawar wani masanin tsirrai.

Bambanci shi ne, shuke-shuke sun taƙaita ne ga abubuwan da aka shuka ko ake shukawa.

Amma botanist kamar yadda aka bayyana shi da Ingilishi, masanin tsirrai kawai ke nan, waɗanda ake shukawa da waɗanda ba shuka su aka yi ko ake yi ba.

Gidan talabijin ƙasar dai ya hasko Malala da iyayenta…

 

Gidan talabijin ƙasar dai ya nuna Malala da iyayenta…

Da Hausa, haskawa na nufin sanya haske a kan wani abu don ganinsa sosai. Shi kuwa abin da ake gani a talabijin, da sinima da sauran allunan da ake kallon wani abu, nunawa ake. Haka kuma hoto tsakanin mutane, nuna shi ake yi, ba haskawa ba.

Misali: Yana nuna fim ɗin Koyon Hausa. Zai nuna masa hoto. An nuna gasar a talabijin.

In an jima kaɗan za ku ji ƙorafin da manoma zuma ke yi a Najeriya.

Za a bunƙasa noman zuma a Najeriya

Ba a noman zuma da sauran halittu masu rai. Kiwon su ake yi.

Abubuwan da ake nomawa su ne tsirrai da ake shukawa ko dasawa. Shi ya sa ma ake wa noman kirari da, na duƙe tsohon ciniki saboda bisa al’ada duƙawa ake yi ana yin shi da fartanya ko garma d.s..

Halittu masu rai kuwa kiwon su ake yi. Misali, kiwon dabbobi, kiwon kaji, kiwon kifi, kiwon zuma d.s.

An kashe sojojin Nigeria dana Kamaru 7 wasu kuma da dama suka samu raunuka inda kuma aka lalala motocin sojojin da dama.

An kashe sojojin Najeriya da na Kamaru bakwai wasu kuma da dama suka samu raunuka, inda kuma aka lalata motocin sojojin da dama.

1. Lalle ne a raba ‘da’ da kuma ‘na’ tunda kalmomi ne daban-daban. Wato za a rubuta, “…sojojin Najeriya da na Kamaru.”

2. Ba daidai ba ne a cikin rubutun Hausa a rubuta sunan Najeriya irin yadda ake rubutawa da Ingilishi.

Mutane za su nemi labaran Hausa ne ta yadda aka nuna masu, da Hausa ko da Ingilishi

3. Galibin alƙalumma daga ɗaya zuwa tara ana rubuta su ne a matsayin kalmomi.

Sai a nemi ƙarin bayani a kan yadda ake rubuta wasu sauran alƙalumman daban-daban.

Shirin makaman nukiliya na Iran

Shirin nukiliya na Iran

Wannan ita ce ma’anar Iran’s nuclear programme.

Idan aka ce shirin Iran na makaman nukiliya tamkar an yi mata ƙage ne.

Na farko, ba fassarar ke nan ba.

Na biyu kuma, a koyaushe Iran ɗin tana jaddada cewa shirinta na  samun makamashi ne kawai, ba makamai ba.

Kuma sunanta zai koma La Republique en Marche, wato The Republic on the Move a Turanci.

To da Hausa fa? Domin an Faransance mai sauraro, an Ingilisance shi, amma ba a gaya masa abin da hakan ke nufi da harshen Hausa da yake sauraro da shi ba.

Tun bayan kafa ƙasar da Kamal Ataturk ya yi….

Wanda ya kafa jumhuriyar Turkiya ta wannan zamani.

Turkiya ƙasa ce da aka kafa tun shekaru aru-aru

Ya ce fari na aukuwa ne a yankunan da ake kwashe tsawon lokaci ana rikici.

Ya ce ƙarancin abinci na aukuwa ne a yankunan da ake kwashe tsawon lokaci ana rikici.

Ma’anar fari wato drought da Ingilishi, ita ce rashin samun ruwan sama tsawon lokaci.

Kalmar Ingilishi ta famine kuma tana nufin fama da ƙarancin abinci ne ba fari ba.

Ɗaya daga cikin mutanen da suka riƙa goyon bayan shari’ar shi ne ɗan kasuwa Charlie Mullins, wanda ya zuba jarin Fam dubu tamanin ga ɓangaren lauyoyin da suka gabatar da ƙarar.

Ɗaya daga cikin mutanen da suka riƙa goyon bayan shari’ar shi ne ɗan kasuwa Charlie Mullins, wanda ya ba da gudummuwar Fam dubu tamanin ga ɓangaren lauyoyin da suka gabatar da ƙarar.

A nan who helped fund na nufin, wanda ya ba da gudummuwar kuɗin gabatar da ƙarar.

Shiga Tsakani

Tsoma baki/tsoma hannu/kutsa kai. Fassarar involvement/intervention ke nan. Shi kuwa ‘shiga tsakani’ mediation ke nan.

Zambiya wadda ruwa ya zagaye baki ɗaya

Zambiya, wadda sam ba ta da iyaka da teku.

Landlocked country na nufin ƙasar da ba ta da iyaka da teku (ruwa)

Kalamin ‘masana’antar fim’ ya zama tuwon-gandu a tsakanin ‘yan fim a Najeriya. Shin daidai ne kuwa ake amfani da shi daga inda aka fassaro shi?

Da Ingilishi akan ce ‘the film industry’ abin da ke nufin ‘sana’ar fim’. Ko ma a ce ‘the advertising industry’ wato ‘sana’ar shirya tallace-tallace’ ga masu so. Haka kuma waɗanda suka sanya wani batu gaba don samun wata galaba, ana kiransa ‘industry’. Misali, ‘the June 12 industry’. Wato sana’ar yayata batun ‘!2 ga Yuni’.

‘Masana’anta’ kuwa ‘factory’ ke nan da Ingilishi.

Da Hausa kuma, idan mutum ya ce ‘masana’anta’, to yana nufin wurin da ake ƙera, ko gina, ko saƙa wani abu ke nan. Misali: masana’antar atamfa, ko bargo ko kwanduna.

Don haka, bisa ma’ana ta Ingilishi da ta Hausa cewa ‘masana’antar fim’ ba daidai ba ne. Sai dai a ce ‘sana’ar fim’.

Ba za ce ‘masana’antar Kannywood’ ba. Sai dai ko a ce ‘Kannywood’ kawai. Hakan ya isa a fahimci abin da ake nufi kamar yadda in an ce ‘Hollywood’ kawai ya isa a san ana nufin sana’ar fim ta Hollywood ke nan, ko masu sana’ar fim ɗin, ba sai an ƙara da ‘industry’ ba. Misali: Kannywood na fitar da finafinai masu kyau. Ko kuma: Sana’ar fim tana ci sosai.

Kiran dakatar da zuwa wasannin Olimpik a Brazil saboda tsoron ɓarkewar cutar zika

‘Kiran dakatar da zuwa wasannin Olimpik a Brazil saboda tsoron bazuwar cutar zika’. Cutar ta riga ta ɓarke, bazuwarta ce ake tsoro

Wakiliyar BBC ta ce, “Kamfanin jirgin saman na Egyptair ya ce jirgin saman ya ɓace ne mil goma kafin ya shiga sararin samaniyar ƙasar ta Masar.”

“Kamfanin jirgin saman na Egyptair ya ce jirgin saman ya ɓace ne mil goma bayan ya shiga sararin samaniyar ƙasar ta Masar.”

Wakiliyar ta ce ne, “The airline says the airplane went missing ten miles into Egyptian airspace.”

Kuma ana danganta ta ne da wata ƙwayar cuta mai suna zika virus

“Cutar zika” (saboda a nan ‘virus’ na nufin ‘cuta’ ne). Tunda akwai kalma ta Hausa, babu dalili mai ƙwari a nan na sanya kalmar Ingilishi.

A Cadi, jami’an tsaro arba’in da bakwai ne suka salwanta, kuma iyalansu suna nuna yatsa ga gwamnati

“Suka ɓata (ɓace)” dai. An fi amfani da salwanta a kan abin da ya ɓata kuma ba a sanya ran gano shi. Wani lokaci ma akan yi amfani da kalmar a matsayin “halaka”. Misali: “Mutane biyar ne suka salwanta a haɗarin mota” yana nufin mutane biyar ne suka rasu.

A ‘yan makwannin nan wasu sun ta bayyana abubuwan da suka auku a Disamban 2015, wato watan shekaran jiya a matsayin ‘bara’

Idan Bahaushe ya ce ‘bara’ yana nufin watanni da yawa da suka kai ko suka kusa goma sha biyu. Don haka kiran watan jiya ko shekaranjiya ‘bara’ zai iya ruɗa mai saurare. In wata bai yi nisa ba gara a ce, ‘Disamban’ ko ‘Nuwamban’ ‘da ya shige’ ko na shekarar da ta ƙare ko shige idan ba ta daɗe da ƙarewa ba.

Yadda za a yi da ‘baɗI’

Ita ma ‘baɗi’ irin hukuncin da aka yi wa ‘bàra’ a sama ya kamata a yi mata. Idan watan da ake magana a kai a shekara mai kamawar a kusa yake, gara a nuna hakan maimakon a ce ‘baɗi ‘ kawai a yi shiru, bayan kuwa wata ɗaya ne, ko biyu ko uku a gaba.

Kuma ana danganta ta ne da wata ƙwayar cuta mai suna zika virus

“Cutar zika” (saboda a nan ‘virus’ na nufin ‘cuta’ ne). Tunda akwai kalma ta Hausa, babu dalili mai ƙwari a nan na sanya kalmar Ingilishi.

Masana’antu sun durƙushe saboda ƙarancin hasken lantarki

“Masana’antu sun durƙushe saboda ƙarancin wutar lantarki”. Amfani da kalmar “wutar” lantarki shi ya fi saboda wutar ta ƙunshi makamashin da ke motsa na’urorin masana’antu don samar da abin da ake buƙata. Aikin haske kuwa bisa al’ada shi ne kore duhu daga wurare – gida, ɗaki, ofis, masana’anta, titi d.s.

Motoci na annashuwa

Na isà, na ƙawà, ko masu tsada (Da Hausa an fi amfani da annashuwa a matsayin farin ciki ko raha. Misali: Na iske shi cikin annashuwa, yai ta ja na da wasa)

Shugaban ƙasar na cikin halin lafiya

Shugaban ƙasar yana nan lafiya (lau)

Fama da rashin hasken wutar lantarki

Fama da rashin wutar lantarki (Idan aka ce haske an rage mata ƙarfi. Ina batun makamashi da take samarwa? Wutar lantarki ta ƙunshi hasken da makamashin)

Reraya

Rera (waƙa rera ta ake yi, ba reraya ba)

Sinadaran toxic

Sinadirai masu guba

Duniyar earth

Duniyarmu (sanya kalmar Ingilishi a nan ba dalili. Za ta ruɗa wanda bai jin Ingilishi ne maimakon ta taimaka masa.

Sony ta haska fim ɗinta

Sony ta nuna fim ɗinta (‘show’ nunawa ke nan da Ingilishi, ‘shine’ kuma shi ne ‘haskawa’)

Faɗa tsakanin mata da miji da ake kira domestic violence

A’a. ‘Domestic violence’ shi ne cin zarafi ta amfani da ƙarfi tsakanin waɗanda ke zaune tare

Dakarun kiyaye zama lafiya

A nan ‘zaman lafiya’ ne daidai tunda ana batu ne a kan wanda ake kiyayewa tsakanin ɓangarori. Amma shi ‘zama lafiya’ za ka iya yin as kai kaɗai. Wato ba tare da rigima da mutane ba.

Antibiotic

A iya kiransa ‘yaƙi-cuta’ wato maganin da ke yaƙar cuta

Pain killer

A iya kiran sa ‘kashe-raɗaɗI’ wato abin da ke kashe zafin ciwo.

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba