Jinsi

Hausa tana bambace kowane abu a kan ko jinsin mace ne ko kuma namiji. Shi ya sa yake da muhimmanci mutum ya fahimci yadda ake gane ko kalma, wadda take sùna ce a nahuwance, jinsin macen ce ko namijin. A aiki da mallaka, namiji yana ɗaukar ‘ya’ da ‘sa’. Misali: Abdu ya zauna kujerarsa. Mace tana ɗaukar 'ta' duka a aiki da mallaka. Misali: Rabi ta zauna a kan kujerarta

 

Kuskure

Daidai

Shugaba Macron ya yi tayi ga Paul Biya da ya shirya wata zama na tattaunawa…

Shugaba Macron ya yi tayi ga Paul Biya da ya shirya wani zama na tattaunawa…

‘Zama’ namiji ne, don haka da namiji za a sifanta shi.

Za a ga alama shuɗi

Za a ga alama shuɗiya.

Jinsin kalmar ‘alama’ na mace ne, don haka da kalmar macen ya kamata a sifanta ta.

Kada a ɗauko kan mace a ɗora wa namiji ko akasin haka.

Mista Egeland ya ce mutane milyan goma sha tara da ke Yamen na buƙatar agajin gaggawa, kuma milyan bakwai daga cikin su na fama da matsanancin yunwa.

Mista Egeland ya ce mutane milyan goma sha tara da ke Yamen na buƙatar agajin gaggawa, kuma milyan bakwai daga cikin su na fama da matsananciyar yunwa.

Jinsin ‘yunwa’ na mace ne ba na namiji ba.

Da Hausa galibin kalmomin da suka ƙare da wasalin ‘a’ jinsin mata ne.

Biri ya haddasa mummunar rikici a Libya

Biri ya haddasa mummunan rikici a Libya

Jinsin ‘rikici’ namiji ne don haka ba za a ce ‘mummunar’ ba.

Galibin kalmomin Hausa da suka ƙare da wasalin ‘a’ mata ne, sauran kuma, galibi maza ne.

Shi ne mutumin Afirka na farko da ya samu lambar yabo na Nobel a kan rubutun adabi a shekarar 1986.

Shi ne mutumin Afirka na farko da ya samu lambar yabo ta Nobel a kan adabi a shekarar 1986.

Tunda har aka ce lambar wannan ya nuna jinsin mace ne ke nan. Kana in aka ce adabi ya isa

Ko me nisan jifa ƙasa zai dawo

Ko me nisan jifa ƙasa za ta dawo.

Jinsin jifa mace ne. Galibin kalmomin da suka ƙare da wasilin ‘a’ jinsinsu na mata ne

Ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ya nuna farin jinin gwamnatin ya ƙaru

‘Ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna farin jinin gwamnatin ya ƙaru’. Jinsin ƙuri’a na mace ne

Na tambaye ta, ko me ya sa kungiyoyi irin tata suka ga ya kamata su shigo wajen sake gina jahar?

“Ƙungiyoyi irin nata”. In dà ƙungiya aka ce, to a nan za a iya amfani da “tata”. Amma a jam’i sai dai a ce “nata”.

Wata máta “ne” wadda

Wata máta “ce” wadda…(lalle a kyautata amfani da jinsi daidai. Abin da jinsin mace ne a sa masa ‘ce’, na namiji kuma a sa masa ‘ne’.

Shugaban Koriya ta Kudu, Park Geun-hye

Shugabar Koriya ta Kudu (mace ce ba namiji ba)

Ranar Litinin ne dai wasu jaridun ƙasar suka wallafa wani talla

Talla (jinsi ne na mace, don haka sai dai a ce ‘wata’ ba wani ba)

Màtàna

Màtàta. Mun ƙara kawo wannan misali ne saboda maida maza mata ko kuma akasin haka, shi ne kuskuren da aka fi yi a wajen magana da Hausa.

Matashiya: Galibin dai kalmomin sunayen abubuwa da suka ƙare da wasalin ‘a’ mata ne, kuma ana sanya masu ‘ta’ don nuna mallaka ko wani aiki. Misali, ‘tunkiyata ce’ ko kuma ‘tunkiya 'ta' girma’. Sai dai duk da yake galibin kalmomin da suka ƙare da wasalin ‘a’ mata ne, akwai wasu kaɗan da suka ƙare da wasalin na ‘a’ amma kuma suka fita zakka, wato suka kasance maza. Misali, ruwa, gida, wata, ƙudà d.s.

Galibin kuma sunayen abubuwa da suka ƙare da wasalin ɗayan waɗannan ‘e, i, o,u’ maza ne, in ban da waɗanda suka fita zakka.

Don haka, ban da kalmomin da suka fita zakkan a kowane jinsi, ɗauki duk sunayen da suka ƙare da wasalin ‘a’ a matsayin mata. Waɗanda kuma suka ƙare da ‘e, i, o, u’ a matsayin maza. A fiye da kashi tisi’in cikin ɗari na lokuta ba za ka yi kuskure ba.

Wannan shi ne sana’armu

‘Sana’a’ kalma ce jinsin mace, don haka sai dai a ce ‘sana’armu ita ce’

Shawarana shi ne

‘Shawara’ kalma ce jinsin mace, don haka ‘shawarata’ za a ce

Abubuwa Biyu Kacal da Za su Gyara Hausarka

Akwai abubuwa biyu da har waɗanda Hausa ta haifa gaba da baya suke yawan kuskure a kai idan sun zo magana da Hausar. Suna kuma yawan maimaita waɗannan kurakurai da ake kama sun da su.

Za kai ta yawan jin su daga bakin ma’aikatan kafofin labarai da mutanen da suke tattaunawa da su.

Idan suka gyara waɗannan ababe biyu, za su inganta Hausarsu ƙwarai da gaske. 

Kurakuran guda biyu

Waɗannan wurare biyu kuwa su ne:

  1. Jirkita jinsi, wato mayar da abu namiji ya koma mace ko akasin haka
  2. Jirkita adadi, wato mayar da jam’i ya koma mufuradi (abu guda)

Bari mu bi su ɗaiɗaya don gane yadda ake yin waɗannan kurakurai da kuma yadda za a gyara su.

A nan za mu batu ne a kan Jirkita Jinsi

Jirkita jinsi

Yadda ake yin kuskuren

  1. “Shin ko wace masaniya hukumkomin Najeriya suke da shi?”
  2. “Kòfin tana da ƙazanta.”

Duka a (a) da (b) a sama akwai kuskure.

A na farko ‘masaniya’ mace ce, an mayar da ita namiji da aka ce, ‘…suke da shi’ maimakon a ce ‘…suke da ita’.

A na biyu ‘kòfi’ namiji ne, amma sai aka mai da shi mace, aka ce, ‘…tana da ƙazanta’, maimakon a ce ‘…yana da ƙazanta’.

Yadda ake bambancewa

Bari mu fara da kuskuren da aka fi yi, shi ne kuwa na mayar da mata, maza.

Mata

Galibin kalmomin Hausa da suka ƙare da ‘a’ mata ne. Misali, masaniya, manuniya, masheƙiya, magudiya, gimbiya, ƙatuwa, mageduwa, munduwa, kwantawa, kishingiɗawa, bugawa, d.s.

Akwai kalmomi kaɗan da suka fita zakka. Ga su da ‘a’ ɗin a ƙarshe amma kuma maza ne.

Misali, gida, noma, wata.

Yayin da waɗannan ɗin ‘yan kaɗan ne, akwai kuma wasu kalmomin na wasu halittu da ake siffanta su a matsayin maza duk da yake sun ƙare ne da wasalin ‘a’.

Misali, dilà, ƙudà, dandà, gòga, d.s.

Maza

Kalmomin da suke maza ne ba su da wuyar ganewa. Galibin kalmomin da suka ƙare da ‘e’, da ‘i’, da ‘o’ da ‘u’ maza ne, in banda kalmomin da ke bayyana halittar da aka san mace ce, kamar ‘mace’ ita kanta ko ‘màge ko sunayen mata irin su Kande.

Misalin kalmomi maza

‘e’ – gyale, lagè, gèfe, gèb’è, hòge

‘i’ – jirgi, makwanci, mabugi, ƙirgi,

‘o’ – ƙòƙo, ròƙo, bàƙo, baiko, bòbò

‘u’ – gudu, ƙugu, runhu, dundu

Don karanta bayanin jirkita adadi, sai a je shafin Mufuradi da Jam’i: http://bbc.in/18muiVu

GA WANNAN SAƘO DA MUKA SAMU

Ina godiya da wannan shafin na BBC HAUSA wanda ke kokarin gyara muna kurakuranmu na yau da kullum a Hausar mu. Sai dai ina jayayya sosai dangane da kasa jinsi wanda aka yi zuwa gida biyu, jinsi kan ya kasu ne zuwa gida uku. Akwai jinsi namiji da jinsin mace da kuma Zulunbu. Akwai wani mutum wanda aka bamu labarin cewar gabansa a shafe yake bashi da kamannun jinsin mata ballantana maza, to irin wannan jinsin su ake kira Zulunbu.

Sani Mohammad Bunza, Kebbi, Najeriya

AMSA

Malam Sani mun yi murna ƙwarai da samun saƙonka. Wannan ya nuna sha’awarka ga harshen Hausa da kuma inganta shi.

Ka ce kana jayayya a kan kasuwar jinsi gida biyu kawai a Hausa kamar yadda muka ce – wato ‘namiji’ da kuma ‘mace’. Har ma ka kawo misali da ‘zulumbu’.

Sai dai Malam Sani, da za ka kawo misali sai ka ce, “Akwai wani mutum….” Ka ga da ka ce haka, ka ba shi jinsin ‘namiji’ ke nan.

Da ma abin da muke son nunawa ke nan. A magana dai, a harshen Hausa, waɗannan jinsuna ne kawai za ka iya bai wa abin da kake magana a kansa, ko da kuwa abin bai da rai. Misali: wata kujera, wani teburi. Kujera ce, teburi ne, wani zulumbu, zulumbu ne. Ko kuma wata zulumbu, zulumbu ce.

Don haka, ko mutum mata-maza ne, ba za ka iya yin irin wannan bayani a kansa ba in ba ka zaɓar masa jinsi ba, ko mace ko namiji – wani mata-maza ko wata mata-maza.

A taƙaice dai, har yanzu ban ji wani jinsi da za ka iya bayyana wani abu da shi ba da Hausa face ya kasance mace ko namiji.

Allah sa wannan amsa ta gamsar.

 

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba