Ɗanɗano: Kuskure a Hausa da kuma Gyara

Wannan fili yana kawo misalai ne na kurakuran da akan tabka wajen magana da Hausa da kuma gyara a kansu. Bisa la’akari da kasancewar ‘yan jarida kunne da idanun jama’a, muna damuwa da kurakuran da ake ji musamman a kafofin watsa labarai. A kan haka ne lokaci-lokaci Sulaiman Ibrahim Katsina na nan BBC yake gabatar da irin waɗannan kurakurai da kuma gyara a kansu don ankarar da junanmu da kuma inganta amfani da wannan harshe da masu magana da shi ke matuƙar alfahari da shi.

Kuskure

Daidai

To kamar su waɗanda ba Musulmi ba, ke nan Musulmin ne su ma suka kashe su…?

A wannan amsa an sanya zargin wani ɓangare. Zai iya yiwuwa su ɗin ne, amma kuma zai iya yiwuwa ‘yan-sanda ne ko soja suka kashe su wajen kwantar da rikici, ko kuma wani abin daban.

Cewa su suka kashe su zai ƙara rura wutar rikici. Cewa ba su suka kashe su ba zai bar zargi a zukata na rashin faɗin gaskiya.

Don haka, gara a yi tambayar ba tare da cusa zargin wani ɓangare ba. Ka ga ba a haɗa wanda ake tambaya da aikin kare wani sashe ba, sai dai ya ya faɗi gaskiyar abin da ya sani kawai.

Ga irin tambayar da ta dace, wadda babu zargi a ciki:

Su mamatan da ba Musulmin ba, mene ne musabbabin mutuwarsu?

A wannan tambaya babu kawo ra’ayi. Abin da ya faru kawai ake son ji.

‘Yan sanda a Afrika ta Kudu sun ce sun gano gawar wani masanin shuke-shuke.

‘Yan sanda a Afrika ta Kudu sun ce sun gano gawar wani masanin tsirrai.

Bambanci shi ne, shuke-shuke sun taƙaita ne ga abubuwan da aka shuka ko ake shukawa.

Amma botanist kamar yadda aka bayyana shi da Ingilishi, masanin tsirrai kawai ke nan, waɗanda ake shukawa da waɗanda ba shuka su aka yi ko ake yi ba

To idan muka je aJumhuriyar ta Nijar…

To idan muka je Jumhuriyar ta Nijar…

Saka ‘a’ da aka yi tsakanin je da jumhuriyar ya maida jumlar bambarakwai.

Ƙarin misalai: Jumlolin “Za mu je Ingila” da “Za mu je Kaduna” duk za su fi daɗi idan ba a ƙara masu ‘a’ ba.

Za ku iya kallon bidiyon a shafinmu na intanet

Za ku iya ganin bidiyon a shafinmu na intanet.

Gara a yi amfani da gani idan bidiyon ko hoto na wani abin baƙin ciki ne da makamancin haka, domin galibi kallon da mutum yake shiryawa don yin sa na jin daɗi ne. Misali, kallon ƙwallo, kallon dambe.

Idan aka je kallon abu, ana murnar yin hakan ke nan. Amma kalmar gani a nan, ‘yar-ba-ruwanmu ce. Shi ya sa gara a ce za a iya ganin bidiyon ko hoton .Halittu masu rai kuwa kiwon su ake yi. Misali, kiwon dabbobi, kiwon kaji, kiwon kifi, kiwon zuma d.s.

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba