Aikin jarida na hazaƙa

Aikin jarida aiki ne na ƙwaƙwalowa da gabatar wa jama’a sabon labari koyaushe. Yana buƙatar iya tallatawa a gaban edita. “Lalle ka zama mai ƙwaƙwar sanin komi yadda har ba za ka iya kallon bangon da babu komi kansa ba ba tare da ka yi mamakin me ya sa ba a rubuta komi a kansa ba.”

Dukkan ‘yan jarida suna son ganin a aikinsu ya zo da wani abu sabo a koyaushe

Dalilin shigarmu aikin jarida shi ne ‘binciko sabon labari’. Aikin jarida aiki ne na faɗa wa jama’a wani abu sabo, wani abu mai jan hanakli. Dukkan ‘yan jarida – ciki har da waɗanda dukkanmu suke burge mu – sukan damu a kan ko suna kawo sabon abu irin yadda ya kamata; daga ina ne labarin gaskiya na gaba zai fito? Aikin jaridar ƙwaƙwalo sabon labari da gabatar da shi cikin fasaha nà buƙatar ƙwarewa. Ƙ’warewa ce da za ka iya koyo, amma da dama daga masu wannan sana’a suna cewa yin aikin jaridar ta irin wannan hanya yana ƙara zama da kamar wuya.

Yanzu tilas ‘yan jarida su fitar da abubuwa da dama fiye da yadda suke yi ko da a ‘yan shekarun baya ɗin nan. Kuma matsin neman ka yi aiki da yawa zai iya sanyawa ka ji cewa aikin na sarrafawa ne kawai ba wai na ganowa ko yin bincike ba. Kana, hamadar bayanan kirki da na jabu, waɗanda a halin yanzu ake iya samu ta yana, suna iya ruɗar da duk wanda ke son ya gano gaskiya.

 

Hanyar kallon lamurra da ɗabi’a

Binciken sabon abu na bukatar aiki mai yawa, da lokaci da aiki da abin da ka binciko ba aikin matsoraci ba ne – aiki ne tuƙuru, ba wai na ‘yan kwanaki kaɗan ba, na koyaushe. Zai iya nufin sauya hanyar kallon al’amurra, ko shakka babu kuma, yana nufin sauyin ɗabi’a.

 

Kwakwar sani

Yayin da nake tsara waɗannan laccoci da bitoci, na yi magana da gwammai daga cikin editocin BBC da suka fi ƙwarewa, da ‘yan rahoto, da mashirya shiri, da masu bincike, na kuma tambaye su dubarori da shawarwari.

A kan lissafin da kowa yake da shi – kuma saman komi – kalmomi biyu ne. Ƙ’waƙwar sani. Idan ba ka mallaki cikakkar ƙwaƙwar sani ba, ɓata lokaci kawai kake yi.

“Idan ba ka zuwa aiki da wani labari da kai ne ka fara gano shi, to ya kamata ka soma jarraba yadda za ka gano labari.”

Ga shawarar ɓalo-ɓalo daga ma’aikatan BBC a Belfast, ɗayansu ya tuna da wani edita da kan:

“...yi tattaki tsawon titi, daga nan sai ya ƙalubalanci saura bisa cewa a tattakin yadi 500 shi ne zai fi kowa samo labarai – (kamar) yawan shara, da tsara ajjiyar ababen hawa, da yawan sabbin motoci, da masu ba da hannu, gidajen shayi da ke cike da mutanen da ke shan sigari saboda an hana sha a wuraren aiki, da lokutan buɗe/rufe shaguna, da masu bara da ke da nasu tarihi, da inda ake gine-gine.

Sau nawa muke wuce gine-gine ba mu kuma tambayar masu aikin “Me kuke ginawa?”

Ga yadda wani editan ya bayyana abin:

 “Lalle ka zama mai ƙwaƙwar sanin komi yadda har ba za ka iya kallon bangon da babu komi kansa ba ba tare da ka yi mamakin me ya sa ba a rubuta komi a kansa ba.”

Tambayi me ya sa...me kuma ba zai sa ba.

Ko ta yaya za ka murɗa kambunka na ƙwaƙwar sanin abubuwa?

Ta hanyar jarrabawa ne, ina tabbatar maka.

Abar da za ka yi ƙoƙarin samu ita ce hanyar kallon al’amurra yadda bai yiwuwa ka saurari wani ko karanta jarida ko mujalla, ko ma tafiya a kan titi ba tare da tunanin ‘wancan abu wani bambarakwai ne’ ba ko kuma ‘Ko wancan game da ainihin mine ne?”

Tilasta wa kanka yin tunanin dukkan tambayoyin da za ka iya, waɗanda abin da ka ganin ko karanta yanzu bai amsa ba.

Jarraba duba a sashen taƙaitattun labarai na jaridu – ɗauki waɗanda suka fi gajarta, ka kuma yi tambaya tare da gano wa kanka amsar dukkan tambayoyi da labarin bai yi ba.

 

Saurari martaninka

Saurari martaninka na farko a kan duk wani labari ko abin da ya auku.

Janye rashin nuna bambanci na ɗan lokaci daga cikin zuciyarka don ka sàmu ka soma tunani. Mine ne martaninka na farko ko tunaninka na farko? Ko wasu mutane ma za su yi tunanin haka? Me zai auku idan ka ƙalubalanci irin wannan martani. Ina zai kai ka?

Ka kuma ci gaba da jarraba hakan a al’amurranka na yau da kullum – ƙarshenta za ka ga wani abu ko ka fahimci wani abin da kowa bai lura ba.

 

Michael Crick na BBC2 Newsnight

“Ko da kana yin wani abu ne na yau da kullum, wanda ga alama ba wani na musamman ba ne, koyaushe ka dinga tambayar “Me zan ce wanda sabo ne a cikin wannan labari?”

Babban abu game da soma tunanin wani sabon abu ta wannan hanyar shi ne ba sai ka san kome ba. Kai dai ka tambayi kanka, ka kuma yi ƙwaƙwar sani. Wani babban edita ya tuna karon farko da aka soma tura shi aiki a lokacin da yake sabon ma’aikaci a wani ƙaramin gidan rediyo a arewa:

“Ban san abin da zan yi ba. Ban san garin ba, ban san kowa ba, ban san inda zan fara ba. Sai Firaminista – Misiz Thatcher ce a lokacin – ta faɗi kafa takunkumin cinikayya a kan Tarayyar Soviet bayan mamayar Afghanistan.

Babu alamar hakan ya shafi irin aikina a lokcin – sai na yi ƙoƙarin ɗaukar kaina a matsayin wani ɗan kasuwa na yankin.

Na buga waya ga shugaban babban kamfanin garin da ya fi sayar da kaya a waje. Yà kaɗu, bugu da ƙari a garin shi babban ɗan jam’iyyar Conservative mai mulki ne. Hira da shi ta kai ga labarai; rahotannin da suka biyo baya su ne kan gaba a jaridun garin da talabijin ɗin yankin.

 

Shigar ma'aikaci

Dan jira yayn da muke binciken ko ka kai ga masadar cikin gida ta BBC

Yi hakuri, mun kasa tabbatar da ko ka sami masadar cikin gida ta BBC

  • Duba don ganin ko sami masadar cikin gida ta BBC
  • Duba ka ga ko adireshin da kake son kaiwa gare shi daidai ne
Rufe ka ci gaba

Mun yi nasarar tabbatar da layi

Rufe ka ci gaba