Shirye-shiryenmu na karshen Mako.
A karshen kowane mako, sashen Hausa na BBC na dauke da shirye-shirye guda ukku. 1. Akwai shiri na musamman a kan harkokin yau da kullum 2. Akwai shirin Amshoshin Takardunku. 3. Akwai kuma shirin Taba Kidi Taba Karatu.
Shiri na musamman.
A kowane mako, Sashen Hausa na BBC, yakan dauki wani al'amari guda domin yin nazari tare da bincike. Wannan shiri ne na tsawon minti goma sha biyu da ake watsa shi ranar Asabar da karfe 0530 agogon GMT, sannan a maimata shi da rana a shirin karfe 1345 agogon GMT.
Amsoshin Takardunku.
Akan amsa tamboyoyi iri-iri wadanda masu saurare su kan aiko a cikin wannan shirin. Akan watsa shi ranar asabar a shirin karfe 1930 agogon GMT. Sannan a maimata shi, ranar lahadi a shirin karfe 1345 agogon GMT.
Taba Kidi Taba Karatu.
Wannan shiri ne da ke dauke da labaru masu ban al'ajabi, daga sassa daban daban na duniya. Ana watsa wannan shiri ranar Lahadi a shirin karfe 0530 agogon GMT, sannan a maimata shi ranar Lahadi da dare, watau a shirin karfe 1930 agogon GMT. A takaice shirye-shiryen karshen mako sune kamar haka. Asabar
| 0530-0600 GMT |
Akwai takaitattun labarun duniya na minti biyu, da cikakkun labarun duniya na minti biyar. Sai kuma rahotanni na akalla minti bakwai, sannan sai shiri na musamman, wanda kan tabo batutuwa iri-iri, na tsawon minti goma sha biyu. |
| 1345-1415 GMT |
Akwai labarun duniya na tsawon akalla minti biyar, da rahotanni na akalla minti bakwai, da kuma maimatawar shiri na musamman. |
| 1930-2000 GMT |
Akwai labarun duniya na akalla minti biyar, da rahotanni na akalla minti goma da kuma shirin Amsoshin Takardunku. |
Lahadi
| 0530-0600 GMT |
Akwai takaitattun labarun duniya na minti biyu, da cikakkun labaran duniya na minti biyar, da rahotanni na akalla minti bakwai, da kuma shirin Taba Kidi Taba karatu. |
| 1345-1415 GMT |
Akwai labarun duniya na akalla minti biyar, da rahotanni na akalla minti bakwai, da kuma maimaitawar shirin Amsoshin Takardunku. |
| 1930-2000 GMT |
Akwai labarun duniya na akalla minti biyar, da rahotanni na akalla minti bakwai, da kuma maimaitawar shirin Taba Kidi Taba Karatu. |
Za'a iya tuntubar mu a wannan addreshin na email: hausa@bbc.co.uk
|