bbc.co.uk navigation

Wasanni

An sabunta: 24 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 18:47 GMT
  • Najeriya ta sha kashi a hannun Peru da ci 1-0 a ci gaba da shirye-shiryen da take yi domin tunkarar wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta 2014.

    24 Mayu, 2012

  • Shugaban kulob din Wigan Dave Whelan ya ce kocin kulob din Roberto Martinez yana ganawa da Liverpool a birnin Miami na Amurka domin kasance wa sabon kocinsu.

    24 Mayu, 2012

  • Shahararren dan tseren kasar Jamaica Usain Bolt, ya ce bashi da wata damuwa game da fafatawa da Dwain Chambers a tseren mita 100.

    24 Mayu, 2012

  • Direban McLaren Jenson Button, ya zamo kan gaba a zagayen farko na gasar tseren motoci ta Grand Prix a birnin Monaco.

    24 Mayu, 2012

  • Rahotanni sun ce Chelsea na shirin sallamar Salomon Kalou da Jose Bosingwa idan kwantiraginsu ta kare a karshen kakar wasanni ta bana.

    24 Mayu, 2012

  • Cristiano Ronaldo ya nuna damuwa kan rashin saka Rio Ferdinand a jerin tawagar 'yan wasan Ingila da za su fafata a gasar cin kofin kasashen Turai ta 2012.

    23 Mayu, 2012

  • Ministan wasannin kasar Kamaru ya ce yana shirin ganawa da manyan 'yan wasan kwallon kasar kafin wasannin share fagen da za su yi a watan Yuni.

    23 Mayu, 2012

  • Dan wasan Aston Villa Darren Bent ya ce kocin Ingila Roy Hodgson ya bashi tabbacin cewa zai shiga cikin shirinsa na gasar cin kofin duniya ta 2014.

    23 Mayu, 2012

  • Shugabar hukumar kula da kwallon kafa ta Burundi, Lydia Nsekera, za ta zamo mace ta farko mamba a kwamitin gudanarwa na hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa.

    22 Mayu, 2012

  • Kungiyar Chelsea ta tabbatar da cewa Didier Drogba ya bar kulob din bayan ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun Turai.

    22 Mayu, 2012

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.