bbc.co.uk navigation

Tsaro a Najeriya

An sabunta: 23 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 17:29 GMT
  • 'Yan Sanda a birnin Sakkwaton Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane biyu a wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a kusa da ofishin mataimakin babban sufetan 'yan sandan kasar da sanyin safiyar yau.

    23 Mayu, 2012

  • Rohotannai daga Najeriya na cewa 'yan sanda sun kama wani mutun dazu a Abuja babban birnin kasar, dauke da makamai da wasu abubuwa masu fashewa.

    21 Mayu, 2012

  • Rundunonin tsaro dake aiki a jihohin Borno da Filato a arewacin Najeriya sun kai samame a wani gida dake Unguwar Rikkos a birnin Jos inda suka ruguza gidan, sannan suka gano muggan makamai ciki har da bama-bamai.

    20 Mayu, 2012

  • Gwamnonin Arewacin Najeriya sun bayyana cewar a shirye suke su dauki matakan bai daya don tunkarar matsalolin tsaro a yankin.

    17 Mayu, 2012

  • Akalla mutane biyu wadanda ake zargin 'yan fashi ne sun mutu bayan wani abu da suke dauke da shi ya fashe a birnin Fatakwal na Najeriya.

    17 Mayu, 2012

  • A jihar Bauchi dake Najeriya an kai hari jiya da dare inda wasu yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kashe mutane biyu.

    11 Mayu, 2012

  • A jihar Filato, dake Najeriya 'yan bindiga sun hallaka mutane bakwai 'yan gida daya a wani kauye dake karamar hukumar Riyom.

    10 Mayu, 2012

  • Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce gano wani sabun shirin, da aka yi na tarwatsa wani jirgin saman Amurka ya nuna cewar 'yan ta'adda na kara gano sabbin dabaru na kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

    8 Mayu, 2012

  • Rahotanni daga garin Biu dake kudancin jihar Borno a Najeriya sunce an samu tarzoma da kone-kone a garin, bayan kisan wasu mutane uku.

    3 Mayu, 2012

  • Jami'an tsaro a jihar Yobe da ke Najeriya sun ce akalla mutane 34 sun mutu, yayin da wasu 29 suka jikkata a harin da aka kai a kasuwar shanu ta garin Potuskum.

    3 Mayu, 2012

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.