Chelsea ta doke Burnley da ci 3-1.

Chelsea win Burnley
Chelsea ta fara gasar bana da kafar dama

Kulob din Chelsea ya doke sabuwar kungiyar Burnley wadda ta dawo gasar Premier bana da ci 3-1 har gida a gasar cin kofin Premier wasan farko.

Dan kwallon Burnley Scott Arfield ne ya fara zura kwallo a ragar Chelsea daga tazara mai nisa, nan take cikin kankanin lokaci Chelsea ta farke kwallo ta hannun Diego Costa.

Andre Schurrle ne ya kara kwallo ta biyu a ragar Burnley lokacin da ya samu tamaula daga Cesc Fabregas, kafin daga baya Branislav Ivanovic ya kara kwallo ta uku a raga.

Didier Drogba da ya shiga sauyin dan wasa a kurarren lokaci ya kusa zura kwallo a raga.

Chelsea za ta buga wasanta na biyu a Stamford Bridge, inda za ta karbi bakuncin Leicester City, wanda Burnley za ta ziyarci kulob din Swansea ranar Asabar.