BBC navigation

Chelsea ta kai wasan kusa da karshe

An sabunta: 8 ga Aprilu, 2014 - An wallafa a 21:10 GMT

Sau biyu Chelsea ta kai wawan hari inda Schurrle da Oscar su ka buga kwallon tana bugun karfen saman raga.

Chelsea ta tsallake rijiya da baya, bayan ta doke PSG 2-0 a Stanford Bridge zuwa wasan kusa da karshe na Zakarun Turai.

A karon farko PSG ta ci Chelsea 3-1 a Paris, da wannan nasarar ta 2-0, jumulla 3-3 ke nan.

Sakamakon kwallon da Chelsea ta jefa a ragar PSG a Paris ta samu galaba.

Andre Schurrle wanda ya shigo daga baya ne ya fara ci wa Chelsea kwallonta a minti na 31.

To amma minti uku ya rage lokaci ya cika na wasan sai Demba Ba ya ceci Chelsea da kwallo ta biyu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.