BBC navigation

Uefa ta amince da sabuwar gasa a 2018

An sabunta: 27 ga Maris, 2014 - An wallafa a 17:30 GMT

Shugaban Uefa Greg Dyke na ganin gasar za ta kayatar

Hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa ta amince da sabuwar gasar kwallon kafa ta tsakanin kasashen nahiyar me suna League of Nations.

Za a fara gasar wadda ta zama ta uku bayan ta kofin duniya da ta kofin kasashen Turai a watan Satumba na 2018.

Har yanzu hukumar ta Uefa kammala shirin yadda gasar za ta kasance amma dai za ta kunshi rukuni-rukuni guda hudu.

Gasar za ta maye gurbin yawancin wasannin sada zumunta na kasashen Turai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.