BBC navigation

Sevilla ta damawa Real Madrid lissafi

An sabunta: 26 ga Maris, 2014 - An wallafa a 23:25 GMT

Real Madrid ta salwantar da damammakin da ta samu a kashin farko na wasan

Sevilla ta damawa Real Madrid lissafi bayan da ci ta 2-1 a gasar La Liga ta Spain.

A wasan da suka yi a gidan Sevilla, Real ce ta fara ci ta hannun Cristino a minti 14 da fara wasa.

Minti biyar tsakani sai C. Bacca ya rama, kuma bayn hutun rabin lokaci ya kara ta biyu a minti na 72.

Real Madrid ita ce ta uku a tebur yanzu da maki 70 a wasanni 30.

Atletico Madrid tana ta daya da maki 73, yayin da Barcelona wadda ta ci Celta de Vigo 3-0 tana ta biyu da maki 72.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.