CAF: An fidda Raja a kofin Zakaru

  • 9 Maris 2014
Caf Champion
An sa ran kungiyar za ta taka rawar gani a gasar bana

An yi waje da kungiyar Raja Casablanca ta Morocco daga gasar cin kofin Zakarun Afirka, bayan da Horoya ta Guinea ta doke ta a bugun fenariti.

Raja, mai rike da kofin karo uku, ta doke Horaya da ci daya mai ban haushi a wasa na biyu da suka kara, wasan farko ma haka aka doke Raja a Guinea, hakan ya sa aka buga fenariti, Horaya ta lashe da ci 5-4.

Enyimba ta Najeriya na cikin manyan kungiyoyin da aka yi waje da su a gasar, inda Real Bamako ta Mali ta doke ta da ci 2-1 a Aba. A wasan farko a Mali Enyimba ce ta lashe da ci daya mai ban haushi.

Hakan na nufin kungiyoyin Najeriya biyu da ke buga gasar a bana an fitar da su: tun farko Kano Pillars ce ta fara fita daga gasar, bayan da Vita ta Congo ta samu kaiwa zagayen gaba a karawar da suka yi a watan jiya.

Kungiyar Zamalek ta Masar da Entente Setif ta Algeria sun kai bantensu, bayan da suka tashi wasanninsu canjaras.