Pardew ya amince da tuhumar FA

  • 6 Maris 2014
Alan Pardew
Kocin ya nemi afuwa sannan kungiyar ta ci shi tarar kudi

Kocin kungiyar Newcastle Alan Pardew ya ce ya yarda da tuhumar da hukumar kwallon Ingila take masa na rashin da'a, lokacin da ya doki dan wasan Hull mai buga tsakiya David Meyler da ka.

Pardew, mai shekaru 52, sai da alkalin wasa ya kora shi cikin 'yan kallo bayan an dawo zagaye na biyu a karawar da suka doke Hull da ci 4-1 a filin wasa na KC.

Kocin ya nemi afuwa bayan an tashi wasa, Newcastle ta ci tararsa £100,000 da kuma gargadinsa da ya gujewa sake faruwar haka a gaba.

Pardew, wanda ya fara kocin kungiyar a shekarar 2010, ya bukaci zaman jin bahasin abinda ya faru.