Reuben ya koma Waasland-Beveren

  • 23 Janairu 2014
Reuben Gabriel
Dan wasan na fatan buga kofin duniya a bana

Kungiyar kwallon kafar Belgium Waasland-Beveren ta dauki dan kwallon Najeriya mai wasan tsakiya Reuben Gabriel bayan da kwangilarsa ta kare a bana.

Ya amince da komawa sabuwar kungiyar ne a lokacin da ake hangen Tottenham da ke buga Premier za ta iya taya shi.

Ya buga atisaye da Spurs har ma ya fara tattaunawa da su, nan take aka bada shi aro.

Reuben mai shekaru 23 ya ce koma kungiyar ne a tsawon shekaru uku da rabi.