BBC navigation

Ba zamu bar 'yan kwaya a Olympics ba

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2013 - An wallafa a 16:39 GMT
Thomas Bach

Shugaban Olympics na Duniya

Shugaban Kwamitin Olympic na Duniya Thomas Bach ya sanarwa da BBC ce wa hukumar sa ta shirya domin dakatar da duk wata kasa da ba ta da ingantaccen tsarin gwada 'yan wasa masu amfani da abubuwan kara kuzari.

Back ya ce duk wata kasa da hukumar kula da ta'ammali da kwayoyi masu kara kuzari ta ambato a jerin marassa kyakkyawan tsarin, zamu dakatar da ita nan take.

Ba mu taba dakatar da wata kasa da ta gaza wajen gwajin amfani da abubuwa masu kara kuzari ba a gasar Olympic.
Sai dai wakilin BBC ya ce ana shirin bai wa hukumar kula da shan kwayoyi masu kara kuzari ta duniya wuka da nama nan da dan lokaci mai zuwa.

Bach da ke halartar taro a Johannesburg kan shan kwayoyi a lokacin wasanni, ya ki amsa tambaya akan Jamaica ko za a dauki mataki a kanta, tunda an sami 'yan wasanta da dama masu shan kwayoyin kara kuzari.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.