BBC navigation

Manchester City ta kori Mancini

An sabunta: 13 ga Mayu, 2013 - An wallafa a 23:41 GMT
Roberto Mancini

A watan Yuli ne Mancini ya sake kulla kwantiragin shekaru biyar da Man City

Manchester City ta kori Roberto Mancini daga matsayin mai horad da 'yan wasanta bayan shekaru uku da rabi da ya yi a kungiyar.

A sanarwar da kungiyar ta bayar ta ce kociyan ya kasa cimma bukatunta in banda kai ta ga Gasar Zakarun Turai ta gaba da ya yi.

Yanzu mataimakinsa Brian Kidd zai rike mukamin a sauran wasanninta biyu na Premier da kuma rangadin wasannin da za su je Amurka a lokacin bazara.

Mancini dan Italiya mai shekaru 48 ya maye gurbin Mark Hughes a watan Disamba na 2009 inda ya dauki kofin FA a 2011 da kuma na Premier a 2012 wanda shi ne babban kofi da kungiyar ta dauka a shekaru 44.

Kociyan Malaga dan kasar Chile Manuel Pellegrini da ake rade radin zai maye gurbinsa ya musanta maganar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.