BBC navigation

Rooney na nan daram a United - Ferguson

An sabunta: 8 ga Maris, 2013 - An wallafa a 17:25 GMT
Wayne Rooney da Ferguson

Akwai rahotonni da dama da ake yadawa kan yadda makomar Rooney za ta kasance

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya yi alkawarin cewa Wayne Rooney zai ci gaba da zama a kulob din har kakar wasanni mai zuwa.

Dan wasan mai shekaru 27, ba a fara wasan da United ta yi da Real Madrid a zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun Turai da shi ba, inda Ferguson ya fara amfani da Danny Welbeck.

Wannan ya haifar da rahotonni da dama a jaridun Ingila cewa United za ta sayar da dan wasan a karshen kakar bana.

"Zai kasance tare da mu badi, " a cewar Ferguson. "Na tabbatar muku da wannan."

Ferguson yana magana ne a karon farko tun bayan da aka baiwa Nani jan kati cikin yanayi mai rudani a wasan da United ta sha kashi da 3-2 bayan wasa gida da waje a hannun Real Madrid.

"Wannan ne karo na uku da aka fitar da mu saboda matakin da alkalin wasa ya dauka, abu ne mai matukar wahala amincewa da wannan hukunci," a cewarsa.

Rooney, wanda rahotonni suka ce yana karbar fan 250,000 a kowanne mako a matsayin albashi, ana alakanta shi da komawa kulob daban-daban, cikin harda Paris Saint-Germain.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.