BBC navigation

CAF 2013: Najeriya da Burkina Faso

An sabunta: 10 ga Fabrairu, 2013 - An wallafa a 18:09 GMT
Sabon Kofin Kwallon Kafa na Kasashen Afirka

Saura kiris a san wanda zai daga Sabon Kofin Kwallon Kafa na Kasashen Afirka

Inda za a fafata: Filin wasa FNB, Soccer City Johannesbur: Lahadi 10 Fabreru: Lokaci 18:30 GMT

Sharhi kai tsaye a shashin Hausa na BBC ta rediyo da kuma Latsa bbchausa.com/mobile da kuma shashin Turanci na Latsa BBC Sport.

Nan gaba a ranar Lahadi ne za a karkare gasar Kwallon Kafa ta cin Kofin Kasashen Afirka, lokacin da Najeriya za ta kara da Burkina Faso, wacce nasararta ta ba-da mamaki a gasar.

A farkon gasar dai Najeriya ta dan yi nauyin jiki amma a sauran wasanninta ta farfado.

Ita kuwa Burkina Faso masharhanta ta baiwa mamaki da salon taka ledarta, kasancewa sau daya ta taba wuce matakin farko a gasar.

A wasan neman matsayi na uku kuwa, ranar Asabar Mali ce ta ci gari bayan da ta lallasa Ghana da ci uku da daya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.