BBC navigation

Guardiola ya koma Bayern Munich

An sabunta: 16 ga Janairu, 2013 - An wallafa a 17:50 GMT
pep guardiola

Pep Guardiola '' burina ne na je gasar premier wata rana''

Kungiyar kwallon kafa ta Jamus Bayern Munich ta sanar cewa tsohon kocin Barcelona Pep Guardiola zai gaji kocinta na yanzu a karshen kakar wasan bana.

Guardiola dan shekara 41 da a ke ganin zai ta fi kungiyar Chelsea ko Manchester City ya sanya hannu a kwantiragin shekaru uku zuwa 2016 a klub din.

Kocin zai maye gurbin mai horadda 'yan Bayern Munich din na yanzu ne Jupp Heynckes wanda zai yi ritaya.

Shugaban kungiyar ta Bayern Karl-Heinz Rummenigge, ya ce , ''Pep Guardiola daya ne daga cikin kociyoyin da su ka fi samun nasara a duniya kuma mun tabbata zai sa ba kawai kungiyar Bayern ta haskaka ba har ma kwallon kafar Jamus baki daya.''

Kafin wannan sanarwar dai, a ranar Laraba Guardiolan ya bayyana cewa wata kungiyar gasar Premier ta Ingila zai koma a nan gaba.

Kungiyar ta Bayern a yanzu dai ita ce ta daya a gasar lig din Jamus, Bundesliga da ratar maki tara, kuma a wata mai zuwa ne za ta kara da Arsenal a wasan 'yan 16 na Kofin zakarun Turai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.