BBC navigation

Kulob din Chelsea ya sayi Demba Ba

An sabunta: 4 ga Janairu, 2013 - An wallafa a 13:14 GMT
Demba ba

Demba ba

Chelsea ta sayi dan wasan Newcastle kuma dan kasar Senegal Demba Ba, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru uku da rabi.

Sai dai ba a bayyana kudin da aka sayi dan wasan ba.

Bayanai sun nuna cewa kwantiragin Ba a Newcastle ta hada da bashi damar tattaunawa da wani klulob idan aka taya shi kan fan miliyan bakwai.

Dan wasan na kasar Senegal, wanda ya koma Newcastle daga West Ham a watan Junin 2011, inda ya maye gurbin
Daniel Sturridge, wanda ya bar Stamford Bridge zuwa Liverpool a wannan makon.

Ba mai shekaru 27 ya zira kwallaye 13 a kakar wasanni ta bana a Newcastle.

Zuwansa Chelsea zai taimaka wurin rage dogaron da aka yi a kan Fernando Torres wanda aka sayo kan fan miliyan 50.

Dan wasan na kasar Spain ya zira kwallaye 14 a kakar bana, sai dai bakwai kawai ya zira a gasar Premier.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.