BBC navigation

Najeriya za ta yi wasan zumunta da Angola a Disamba

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:28 GMT

Shugaban NFF, Aminu Maigari

Hukumar kwallon kafar Najeriya, NFF ta ce 'yan wasan kasar za su buga wasan sada zumunta da takwarorinsu na kasar Angola a Portugal a watan Disamba.

NFF ta kara da cewa tana tattaunawa da kasashen Morocco da Cape Verde wadanda su ma za ta buga wasan share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Afirka da su a kasar ta Portugal.

Jami'in NFF, Ademola Olajire, ya shaidawa BBC cewa, "Najeriya za ta buga wasa da Angola a Faro lokacin da za mu je sansanin wasa na kasashen Turai. Za mu sanar da ranar da za a yi wasan.Dukkanin bangarorin sun dauki wannan wasa da muhimmanci, don haka ana tattaunawa dangane da ranar da ta fi dacewa a tsayar don buga wasan".

Olajire ya kara da cewa 'yan wasan kasar na shiryawa sosai don ganin ba su bai wa magoya bayansu kunya lokacin buga wasannin ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.