
Tsohon kyaftin din Ingila, John Terry
Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta fara sauraron bahasi game da halayyar da John Terry ya nuna ga dan wasan QPR, Anton Ferdinand.
Ana zargin Terry da furta kalaman cin mutunci ko nuna halayya mara kyau ga Ferdinand, a gasar da aka buga ranar 23 ga watan Octobar shekarar da ta wuce.
Kyaftin din Chelsea wanda kuma ya musanta zargin ya sanar da cewa zai yi ritaya daga buga wa Ingila wasa a jajiberin jin bahasin.
A watan Julin da ya gabata wata kotun majistire a Westminster ta wanke John Terry, daga zargin nuna wa Ferdinand wariyar launin fata.
Sai dai mako biyu bayan nan hukumar sa ido a wasan kwallon kafa ta kasar ta sake tuhumar Terry.
Za a kwashe kwana biyu ana sauraron bahasin da ake yi a gaban hukumar mai zaman kanta a Wembley.












