
Abdelilah Benkirane na Morocco
An nada Rabat Boss Rachid Taoussi a matsayin sabon kochiyan kasar Morocco dan ya maye gurbin Eric Gerets dan kasar Belgium wanda aka sallame shi makon da ya gabata.
An sallami Gerets ne bayan da Kungiyar kwallon kafa ta Mozambique ta lallasa Atlas Lions ta Morocco da ci biyu ba ko daya a wasan neman futowar gasar cin kofin Nahiyar Afrika.
Tsohon mai tsaron gida na Atlas Lions Badou Zaki wanda ya ja ragamar Kungiyar a gasar cin Kofin Afrika a shekara ta dubu biyu da hudu shi ma an danganta shi da mukamin.
Tsohon Kochiyan Morocco Mohammed Fakhir wanda ya ja ragamar kungiyar a shekara ta dubu biyu da shida a gasar cin kofin Afrika da kuma Aziz El Amri wanda ya horas da Moghreb Tetouan zuwa gasar Champions League na Morocco kakar bara duka an yi tsammanin za su iya samun mukamin.













