
Wasu 'yan gaban Belgium
Kochiyan Belgium Tom Saintfiet ya nuna rashin jin dadin sa da korar sa da Kungiyar kwallon kafa ta Yanga ta yi bayan wasanni biyu kachal da ya jagoranta
Kulab din Yanga dai ya fara wasan ne da cancaras inda a wasa na biyu kuma aka yi nasara akan sa, abinda Santfiet ya ce bai kai a yi masa hukunci ba a matsayin sa na mai horas wa.
Ya ce bayan wasanni biyu "ba za ka ce mun fara da rashin sa'a ba, Mourinho wanda yake da gogaggun 'yan wasa a Spain ba ko wane wasa yake nasara ba."
Tsohon kochiyan Ethiopia da Namibia ya kadu da yadda ya rasa aikin sa.












