
Wasan Ingila da Sweden
'Yar wasan kwallon kafa ta mata ta Ingila, Rachel Yankey na fatan tawagar kulab din za ta yi abin mamaki a gasar cin kofin Nahiyar Turai bayan da suka samu nasarar shiga gasar a jiya inda suka ci Croatia da ci uku ba ko daya.
Yankey ta ce fitowar da suka yi nada mahimmancin gaske. A cewar ta za su tabbatar wa da mutane cewa suna da gogewar da za su fara cin kambu.
Kulab din Ingilar dai Germany ta ci su shida da biyu a wasan karshe na gasar a shekara ta dubu biyu da tara amma yanzu Ingilar na son samun nasarar gasar.
Kwallon da Yankey ta taka a wasan Croatia ya nuna fifikon tarihin wasa da suke kafada da kafada da Gillian Coultard.













