
Di Matteo
Kochiyan Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roberto Di Matteo ya ce samun nasarar kambun Champions League zai yi wuya bana idan aka kwatanta da bara.
Kochiyan ya kara da cewa a rukunin da suke dukanninsu masu kambun Champions din ne daga kasashen Italiya da Ukraine da kuma Denmark saboda haka samun nasarar akwai dan karan wahala.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dai ta yi gasar Champions League karo goma sha daya kuma ta bayyana a gasar sau goma a jere a baya bayannan.
Chelsea din dai ta samu nasarar gasar ta Champions League a karon farko a tarihin kulab din lokacin da suka doke Bayern Munich a bugun daga kai sai mai tsaron gida a gasar kakar bara, amma Di Matteo ya takar kare cewa lokaci yayi da za su matsa gaba.












