
Mark Hughes
Kochiyan kulab din Queens Park Rangers, Mark Hughes, ya ce yana fatan a daina gaisuwa tsakanin 'yan wasa kafin a yi wasan saboda abin wani dan wasa ya jisga takwaransa a lokacin da ya kamata su gaisa.
Anton Ferdinand ne dai ya jisga JohnTerry ya ki gaisawa da shi a lokacin da John Terry ya zo su gaisa abinda ya jawo akaita buga labarin a kafafa yada labarai.
Mark Hughes bayan da aka tashi daga wasan tsakanin QPR da kuma Chelsea babu ci; ya ce yana fatan dai wannan zai zama na karshe.
Duk kannin Kungiyar kwallon kafar sun samu damar da za su zura kwallo a raga amma hakan bata samu ba.













