
Manchester United
Kulab din Manchester United ya soki lamirin wakoki da ihu marasa dadi ga kulab din Liverpool a wasa da Manchester United tayi da Wigan inda ta ci Wigan hudu ba ko daya.
Masu son kulab din dai sun kekashe kunnuwan su ga kiran da Kochiyan Kulab din Manchester United Sir Alex Fergusson ya yi musu cewa akwan tar da hankali kan rahoton da ya futo na Hillsborough.
Kochiyan Alex Fergusson ya ce Kulab din dai ya futar da matsayar sa kuma ya rage ga masu son kulab din su nuna ladabin su ga matsayin kulab din kan batun.
Sai dai Kungiyar masu son kulab din Manchester United sun futar da wata sanarwa suna cewa sun yarda da maganar Sir Alex Fergusson dari bisa dari, amma acewar su wakar da aka ji lokacin wasa da Wigan ba wai akan batun Hillsborough ba ne.
An dai wanke masu son kulab din Liverpool kan zargin da ake musu na mutuwar mutane casa'in da shida a shekarar alif dari tara da tamanin da tara.


















