Tsohon mai rike da kambun wasan dambe na duniya na bangaren masu nauyi, Ricky Hatton na gab da komowa fagen wasan dambe, hakan ya biyo bayan bayyanar da yayi a gaban jami'an wasan dambe inda ya nemi a maido masa da lasisinsa.

Ricky Hatton dan wasan dambe
Dan wasan mai shekaru 33 ya halarci ganawar hukumar dake sa ido a kan wasan dambe ta Birtaniya, gabbannin taron manema labarai da za a yi a ranar Juma'a.
Babban sakataran hukumar, Robert Smith ya shaidawa BBC cewa " Za a mayar masa da lasisin nasa da zarar an kammala binciken lafiyarsa".
"Ya yi magana lafiya kalau kuma da alamun yana cikin koshin lafiya, sannan kuma yana so a kara bashi wata dama da 'yan kallo za su jinjina masa."
Hatton wanda aka yi wa lakabi da The Hitman a turance bai sake shiga fagen dambe ba tun lokacin da Manny Pacquiao ya naushe shi ya suma a watan Mayu na shekarar 2009.
A shekarar 2010 hukumar kula da wasan damben Birtaniya ta karbe kambun Hatton, saboda zargin da aka yi masa na amfani da hodar ibilis.













