
Bikin tunawa da mutuwar masoya wasan kwallo a Hillsborough
Iyalan masoya wasan kwallon da suka mutu a Hillsborough a shekarar 1989, sun bukaci a mika batun kotu don hukunta wadanda ke da laifi a bala'in.
Hakan ya biyo bayan wani rahoton da aka fitar wanda ya nuna cewa akwai sakaci a al'amarin.
Rahoton dai mai zaman kansa ya gano cewa 'yan sanda sun yi sakaci wajen ceton mutane 96 da aka tattake, kuma sun sauya bayanan shaidu, inda suka dora laifin a kan masoyan kulob din Liverpool.
Wani mutum, Trevor Hicks wanda 'ya'yansa mata biyu suka mutu lamarin ya ce, yanzu lokaci ya yi da gwamnatin za ta gyara al'amura.
Haka ma shugaban 'yan sanda a kudancin Yorkshire, David Crompton ya ce, idan 'yan sanda sun karya doka to ya zama dole a hukunta su.
Firai ministan Birtaniya, David Cameron ya ce atoni janar Dominic Grieve, zai sake duba rahoton cikin dan karamin lokaci, don tantance ko ya kamata a mika batun babbar kotu a kasar ko kuma a sake wani bincike.













