
Dan wasan Manchester City David Silva
Kulob din Manchester City yana shirin baiwa dan wasansa David Silva sabon kwantaragin shekaru 5 domin kawarda sha'awarda Real Madrid suka nuna a kansa.
Jami'an Kulob din na City sun gana har sau 3 da mashawartan dan wasan dan kasar Spain a wannan zangon wasannin; kuma sun amince kan wasu sharudda da za su saka shi cikin jerin 'yan wasanda suka fi samun albashi mafi tsoka a kungiyar.
Sabanin wasu rahotannin, tattaunawar ta tafi a tsanake tsakanin bangarorin biyu kuma zakarun na gasar Premier League sun amince da biyansa Fan 240,000 a mako; da hakan kuma sun hakikance cewar sun kakkabe hannuwan Real madrid daga dan wasan.
Kwantaragin Silva da Kulob din na City ta yanzu dai za ta kare ne a 2014 kuma jami'an Real Madrid sun sakawa dan wasan mai shekaru 26 ido a duk tsawo wannan zangon.













