
Wasu daga cikin 'yan tawagar magoya bayan kungiyar Kwallon kafa ta kasar Kamaru
Jami'an tsaro dauke da makamai sun killace ginin ofishin hukumar wasan Kwallon kafa ta kasar Kamaru bayan wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafar kasar sun yi barazanar wasashe ofisoshinta; sakamakon doke kasar da aka yi a karshen mako.
Kungiyar kwallon kafa ta kasar ta Indomitable Lions wadda ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika har sau uku, na cikin hadarin rasa damar shiga gasar ta badi wadda za a yi a Afrika ta kudu; bayan shan kashi da ci 2-0 hannun 'yar kankanuwar kasar Cape Verde ranar assabar, a wasan farko na zagayen karshe na gasar neman cancanta shiga gasar ta cin kofin nahiyar Afrika.
Mogaya bayan kungiyar wadanda ke cike da fushi sun yi zanga-zanga a wajen ofisoshin hukumar bayan gama wasan wanda suke ganin sakamakon sa a zaman cin fuska ga kasar.
Dole ne dai Kamaru ta lashe wasa na biyu da za su buga da Cape Verde din a watan gobe da a kalla ci ukku kafin ta samu cancantar shiga gasar.













