
John Terry yana mamakin ba shi jan kati
Mai tsaro gida na Ingila John Terry ba zai samu damar buga wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da kasarsa za ta buga da Ukraine ba ranar Talata.
Terry wanda Kyaftin din Chelsea ne dai ya kasa warkewa daga wani rauninda ya samu a kafarsa ne, sa'adda Ingila din ta doke Maldove da ci 5-0 ranar Jumu'a.
Akwai yiwuwar za a maye gurbinsa da takwaransa da kulob din Chelsea Gary Cahill, kodayake shima mai tsaron gidan Everton Phil Jagielka yana cikin wadanda za a iya zaba domin tsayawa tare da Joleon Lescott wajen tsaron gidan Ingila a wasan.
Dama dai Koch Roy Hodgson ya rasa 'yan wasa uku daga cikin wadanda ya zabo domin buga wasa da Ukraine din; da suka hada Ashley Cole, da Adam Johnson da kuma Wayne Rooney sakamakon raunukkanda suke da su.












