
Dan wasan Manchester United Phil Jones
Manchester United ta sanarda cewar mai tsaron gidanta Phil Jones zai dauki makonni 8 ba tare da ya buga wasa ba bayanda aka yi masa tiyata a gwiwa.
Ya zuwa yanzu dai Jones dan shekaru 20 bai buga wasa ko daya ba a wannan zangon saboda rauninda ya samu a bayansa yayin wasannin share fagen shiga zango;yayinda kuma ya samu wannan sabon raunin wurin daukar horo a farkon makonnan.
Kakakin Kulod din yace Jones wanda shine na biyar daga cikin 'yan wasan kungiyar ba su buga wasa saboda raunukka, zai bukaci makonni 6 kafin ya warke.
Dan wasan dan kasar Ingila dai zai rasa damar buga wasanni shidda na Premier league da kuma wasanni biyu na gasar Zakarrun turai da Manchester United za ta buga tsakanin watannin Satumba da Oktoba; sai dai manajan kungiyar Sir Alex Ferguson yana fatan zai dawo buga wasa sa'adda Arsenal za ta ziyarci Old-Trafford ranar 3 ga watan Nuwamba.













