
Jerin 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya wato Super Eagles
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Stephen Keshi ya fadawa 'yan wasansa da kakkausan lafazi cewar sun nuna rashin kwarewa a yadda suka buga wasa da kasar Laberiya.
'yan wasan na Super Eagles dai sun tashi kunnen-doki ci 2-2 ne da Lone stars na Laberiya a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika ranar Assabar.
Wata sanarwa daga Jami'in watsa labarai na kungiyar Ben Alaiya tace Keshi wanda ya yiwa 'yan wasan jawabi jim kadan bayan tashi wasan a filin wasa na Samuel Doe dake birnin Monrovia, yace ba za a kara amincewa da irin wannan taka rawar ba.
Sanarwar wadda aka fitar ranar lahadi bayan da tawagar Najeriya ta dawo gida; ta ambato kocin yana cewa: '' Zan fi farin ciki idan 'yan wasa za su yi zamansu a inda suke su ce ba za su samu zuwa, ba bisa ga su zo su nuna wa 'yan Najeriya cewar ba mu san abinda muke yi ba.''


















