
Roy Hodgson Kocin kasar Ingila
Manajan Kungiyar Kwallon kafa ta kasar Ingila Roy Hodgson yace fitar da wasu 'yan wasansa suka yi daga jerin wadanda za su buga wasa ya wargaza shirinda yake na fuskantar kasar Moldova a gasar neman cancantar shiga gasar cin kofi duniya.
Wayne Rooney, da Andy Carroll da kuma Adam Johnson duk ba za su samu buga wasan da za buga ranar Jumu'a ba saboda raunukkan da suke da;kuma mai tsaron gida Ashley Cole ke da rauni a gwiwarsa.
Sai dai Hugson ya samu kwarin gwiwa da dawowar dan wasan tsakiya Michael Carrick cikin tawagar da za ta buga wasan.
''Ba karamin ci-baya ba ne mutum ya rasa hazikan 'yan wasan da ya zabo, amma mun zabo 'yan wasan da yawa domin cike gurbin'' Inji Hodgson.













