
Dan wasan Chelsea Ashley Cole
Dan wasan bayan Chelsea Ashley Cole na shirin barin kulob din bayan yayi masa tayin tsawaita kwantaraginsa da shekara daya kawai.
Mai tsaron gidan na Ingila dai na cikin shekarar karshene ta kwantaraginsa a kungiyar kuma a watan Janairu zai iya tafiya wani Kulob din kyauta.
Wata majiya a kungiyar ta Chelsea Manajanta Roman Abramovich ya saka wata doka cewar duk dan wasanda ya wuce shekaru 30 da haihuwa za a iya tsawaita kwantaraginsa ne da shekara daya kawai.
Cole mai shekaru 31 ya bar kungiyar Arsenal ne a shekara ta 2006 bayanda yace ya kusan yin hadari da motarsa lokacinda kungiyar ta yi masa tayin rika biyansa fam 55,000 a kowane mako.


















